Zaben 2023: Rikici Yayin Da Adams Oshiomhole Ya Gabatar Da Babban Zargi Kan Peter Obi

Zaben 2023: Rikici Yayin Da Adams Oshiomhole Ya Gabatar Da Babban Zargi Kan Peter Obi

  • An bayyana Peter Obi dan takarar shugaban kasa na Labour Party a matsayin wanda ya fi kowa kawo rashin ayyukan yi a Najeriya
  • Tsohon gwamnan jihar Edo kuma tsohon shugaban jam'iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole ya yi wa Obi wannan fasarar
  • Oshiomhole ya yi ikirarin cewa Obi mai kawo rashin ayyukan yi a kasa ne saboda kasuwancinsa na shigo daga kaya daga kasashen waje

Jihar Edo - Tsohon shugaban jam'iyyar All Progressives Congress, APC, na kasa, Adams Oshiomhole ya zargi dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar LP, Peter Obi, da kasancewa babban mai kawo rashin ayyukan yi a Najeriya, Daily Trust ta rahoto.

Oshiomhole yayin jawabinsa wurin kaddamar da kamfen dinsa na neman kujerar sanata na mazabar Edo ta Arewa a karkashin jam'iyyar APC ya ce Obi ya bada gudunmawa wurin rashin aikin yi a kasar kasancewarsa mai shigo da kayan masarufi daga kasashen waje.

Kara karanta wannan

Obi: Zan Daina Kamfen Idan Wani Zai Iya Kawo Hujjar Cewa Na Karbi kyautar Fili A Matsayin Gwamnan Anambra

Obi da Oshiomhole
Zaben 2023: Rikici Yayin Da Adams Oshiomhole Ya Gabatar Da Zargi Mai Tsanani Kan Peter Obi. Hoto: Vanguard
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Tsohon gwamnan na jihar Edo ya ce kasancewar Obi ne da ke kanti mafi girma a Abuja wanda ke siyo innabi, tufafi da wasu kayayyaki daga kasar waje, shi (Obi) yana bada gudunmawa wurin karya darajar naira, rahoton Ripples Nigeria.

Kalamansa:

"Obi ke da kanti mafi girma a Abuja kuma duk kayan da aka sayarwa a wurin daga kasashen waje aka shigo da su, don haka idan yana sayar da innabi na kasar waje, tufafi da wasu kayayyakin, yana bada gudumawa kan dalilin da yasa Najeriya ke kasa saboda yana samar da aiki a kasar waje kuma yana shigo da rashin aikin yi Najeriya."

Peter Obi dan kasuwa ne kuma ya rike mukamin shugaba a daya cikin bankunan zamani a Najeriya.

Shine kuma mammalakin fitaccen kantin Next Cash and Carry da ke Jabi a Abuja, babban birnin tarayya.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Ban Rufe Kofar Sulhu Ba, Atiku Ya Bawa Wike Amsa

Kantin ya lalace sakamakon gobara a watan Disambar 2021 kuma tun lokacin ya dena aiki.

Peter Obi Ya Ce Ko yayan Cikinsa Ba Su Yarda Da Shi Idan Ya Yi Alkawari, Mutane Sun Yi Martani

A bangare guda, Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar LP, yana shan suka a soshiyal midiya saboda amsar da ya bada kan tambayar da aka masa game da yadda zai farfado da lantarki a Najeriya.

Mai gabatar da shirye-shirye na Arise TV ya ce wannan shine dalilin da yasa ya kamata dan takarar LP din ya fitar da manufofinsa ga kasar a rubuce don mutane su gani su yi nazari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164