Obi: Zan Daina Kamfen Idan Wani Zai Iya Kawo Hujjar Cewa Na Karbi kyautar Fili A Matsayin Gwamnan Anambra

Obi: Zan Daina Kamfen Idan Wani Zai Iya Kawo Hujjar Cewa Na Karbi kyautar Fili A Matsayin Gwamnan Anambra

  • Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party (LP) ya ce zai dena kamfen idan za a iya kawo hujjar cewa ya karbi fili daga jiha lokacin yana gwamna
  • Obi ya fadi hakan ne a matsayin amsa kan tambayar da sarkin Benin, Oba Ewuare II ya masa kan wani takarda da ke nuna an bashi fili amma ya ki karba
  • Tsohon gwamnan na jihar Anambra ya bayyana hakan ne yayin da ya ziyarci fadan Sarkin Benin, Oba Ewuare II a jihar Edo lokacin da ya tafi yakin neman zaben a jihar

Benin - Dan takarar shugaban kasa na Labour Party, LP, Peter Obi ya ce zai dena kamfen dinsa na zaben 2023 idan wani zai iya kawo hujjar cewa ya karbi kyautan fili a matsayin gwamnan jihar Anambra.

Kara karanta wannan

Yadda Wata Budurwa Yar Shekara 18 Ta Kashe Jaririnta Da Wuka Bisa Shawarar Mahaifiyarta Yar Shekara 60

Dan shekarar 61 kuma tsohon gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Juma'a a fadar sarkin Benin, Oba Ewuare II, jihar Edo, rahoton Channels TV.

Peter Obi
Obi: Zan Daina Kamfen Idan Wani Zai Iya Kawo Hujjar Cewa Na Karbi kyautar Fili A Matsayin Gwamnan Anambra. Hoto: @ChannelsTV.
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Dan takarar shugaban kasar na LP ya ziyarci sarkin na Benin ne lokacin da shi da tawagarsa suka tafi yin kamfen a Edo gabanin zaben Fabrairu.

Obi ya yi farazanar fasa kamfen dinsa idan an kawo hujjar ya karbi kyautar fili a Anambra lokacin yana gwamna

Da ya ke tarbar dan siyasan, Oba Ewuare II ya yi amfani da damar ya yi karin haske kan wani takarda inda Obi ya ki karbar fili daga gwamnatin Jihar Anambra lokacin yana gwamna, Olisa TV ta rahoto.

Sarkin mai daraja ta daya ya ce:

"Mai girma, wani ya nuna min wasika inda aka baka fili a jihar ka amma ka mayar da shi cewa baka bukata; cewa hidima ka zo yi. Haka ne?"

Kara karanta wannan

Rabin Albashi: Badaru Ya Bayyana Kokarin da Suke Tsakanin ASUU da FG

Obi ya bada amsa:

"Haka ya ke".

Dan takarar shugaban kasar na LP ya ce:

"Idan akwai wanda ya ga filin da aka bani, ko matata ko wani cikin iyali ne, kai tsaye ko a fakaice lokacin da na ke gwamna, zan daina kamfen."

Zaben 2023: Peter Obi Ya Ce Ko Ƴaƴan Cikinsa Ba Su Yarda Da Shi Idan Ya Yi Alƙawari, Mutane Sun Yi Martani

Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na LP, yana shan suka a soshiyal midiya saboda amsar da ya bada kan tambayar da aka masa game da yadda zai farfado da lantarki a Najeriya.

Mai gabatar da shirye-shirye a Arise TV ya ce wannan shine dalilin da yasa ya kamata dan takarar LP din ya fitar da manufofinsa ga kasar a rubuce don mutane su gani su yi nazari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel