NNPP: Jam’iyyar su Kwankwaso Ta Shiga Cikin ‘Rigimar’ Atiku Abubakar da ‘Yan APC

NNPP: Jam’iyyar su Kwankwaso Ta Shiga Cikin ‘Rigimar’ Atiku Abubakar da ‘Yan APC

  • Jam’iyyar New Nigerian People’s Party (NNPP) tayi tir da abin da ya faru da Atiku Abubakar a Borno
  • Ana zargin wasu tsageru sun kai hari ga tawagar ‘dan takaran shugaban kasar da ya je kamfe a Maiduguri
  • Kakakin NNPP a Najeriya, Dr. Agbo Major yace akwai bukatar shugaban kasa ya ja-kunnen Gwamnoni

Abuja - Jam’iyyar hamayya ta NNPP tayi kira ga Mai girma shugaba Muhammadu Buhari ya ja-kunnen gwamnonin jihohin jam’iyyar APC mai mulki.

Vanguard tace wannan gargadi ya zo ne bayan harin da wasu tsageru suka kai wa tawagar da ke tare da Atiku Abubakar mai takarar shugabancin kasa.

Ana zargin an kai wa magoya bayan jam’iyyar PDP da ke tare Alhaji Atiku Abubakar hari a Borno. Jam'iyyar APC ta musanya wannan zargi da ake yi mata.

Kara karanta wannan

‘Dan Takarar Gwamnan PDP na Borno Ya Fallasa Yadda Harin da Aka Kaiwa Tawagar Atiku Ya Faru

A ranar Alhamis, Jam’iyyar NNPP ta bakin Sakataren yada labaranta na kasa, Dr. Agbo Major ta fitar da jawabi na musamman game da abin da ya faru.

A jawabin da Dr. Agbo Major ya sa hannu a madadin jam’iyya mai kayan marmari, yace akwai bukatar shugaban kasa ya tsoma bakinsa a kan batun.

Kakakin NNPP ya ba shugaban Najeriya shawara ya gargadi gwamnonin jam’iyyar APC da su guji yin abin da zai kawo matsala a tafiyar siyasar kasar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Atiku Abubakar
'Dan takaran PDP, Atiku Abubakar a Minna Hoto: Atiku.org
Asali: Facebook

Dole ayi Allah-wadai - NNPP

Channels tace jam’iyyar NNPP tayi Allah-wadai da harin da aka kai wa ‘ya ‘yan PDP a Maiduguri, tace an yi haka ne da nufin kawo tashin-tashina a 2023.

Har ila yau, jam’iyyar tayi kira ga gwamnati da mutanen Najeriya duk su fito su yi tir da abin ya faru, wanda ta kira da jahilci, takalar fada da kuma zalunci.

Kara karanta wannan

Tinubu: APC Tayi Kuskure Wajen Tsaida ‘Dan Takaran Shugaban Kasa Inji Kwankwaso

Agbo yace wadanda suka yi wannan abin ashha, masu adawa da tsarin damukaradiyya ne, masu neman kawo siyasar daba a maimakon zaman lafiya.

Ba yau aka soma ba - Agbo

Jam’iyyar NNPP ta kasa tace abin da ya faru a makon da ya shude ya nuna bakin halin APC a Borno na yin fito-na-fito da duk wata jam’iyyar hamayya.

A cewar Agbo, a watan Agustan nan an yi wa NNPP irin wannan yayin da Rabiu Kwankwaso (FNSE), Ph.D ya je bude sakatariyyar jam’iyya da ke jihar.

Jam’iyyar adawar tana zargin Gwamna Babagana Zulum ya ba ‘yan sanda umarnin rufe mata sakatariya, saboda ya tsora da farin jinin Sanata Kwankwaso.

Za a iya hana Tinubu takara?

A jiya aka ji labari Daniel Bwala wanda yana cikin Kakakin Alhaji Atiku Abubakar a zaben 2023 yace takarar Bola Tinubu tana fuskantar babban hadari.

Mai magana da yawun bakin na Atiku Abubakar yace idan zargin badakalar kwayoyin da ake yi wa Tinubu ta je kotu, magana za ta iya canzawa.

Kara karanta wannan

2023: Kwankwaso ya ce ya ji dadin yadda APC da APC ba su ba wasu 'yan siyasa biyu tikitin gaje Buhari ba

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng