Dan Takarar Shugaban Kasa Na PDP, Atiku Abubakar Ya Gana da IBB a Minna
- Yanzu muke samun labarin wata ziyara da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya kai birnin Minna ta jihar Neja
- An ruwaito cewa, Atiku ya shiga ganawa da tsohon shugaban Najeriya na mulkin soja, Jamar Ibrahim Badamasi Babangida mai ritaya
- Ana kyautata zaton za su tattauna yadda za a shawo kan rikicin cikin gida da jam'iyyar PDP ke fuskanta a 'yan watannin nan
Minna, jihar Neja - Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya kai ziyara birnin Minna a jihar Neja, inda ya gana da tsohon shugaban Najeriya na mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida mai ritaya.
A cewar rahoton The Nation, Atiku ya isa Minna ne da misalin karfe 12:45 na rana, inda aka zarce dashi kai tsaye zuwa gidan IBB.
Atiku ya dura jihar ne tare da abokin takararsa; gwamna Ifeanyi Okowa, daraktansa na kamfen; gwamna Aminu Tambuwal da gwamnan Taraba, Darius Ishaku.
Hakazalika da tsohon gwamnan Adamawa; sanata Boni Haruna, tsohon gwamnan Imo Emeka Ihedioaha, tsohon gwamnan Jigawa, Sule Lamido da kuma tsohon gwamnan Neja Dr Mu'azu Babangida Aliyu.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Sauran kuma sun hada sanata Ben Obi, sanata Dino Melaye, sanata Abdul Ningi da kuma shugaban PDP na Neja da dai sauran jiga-jigan PDP.
Akwai kuma manyan jiga-jigan PDP da dama da suka samu halartar wannan ziyara ga tsohon jigon kasa.
IBB zai shiga tsakanin don warware rikicin PDP
A wani rahoton jaridar Leadership, majiya ta bayyana cewa, Atiku Abubakar zai gana da tsohon shugaban kasan ne don kawo karshen rikicin da PDP da gwamnonin G-5 ke kara rurutawa.
Ana kyautata zaton IBB zai zauna da gwamnonin G-5 dinne domin jin ta bakinsu tare da ba su shawarin dawo da zaman lafiya a jam'iyyar.
A makon nan ne dai IBB ya gana da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Bola Ahmad Tinubu, yau kuma ya gana da na PDP.
Atiku kai ziyara jihar Borno, an farmaki tawagarsa
Kafin ziyararsa ta jihar Neja, ya ziyarci jihar Borno inda wasu 'yan daba suka farmaki tawagar ayarinsa tare da raunata mutanensa sama 70.
An kuma yi kaca-kaca da motoci da dama na PDP, lamarin da ya jawo cece-kuce a tsakanin 'yan siyasar kasar nan.
Asali: Legit.ng