Gwamnan Bala Ya Yi Magana Kan Wasikar da Ya Aika Wa PDP da Ganawa da Atiku
- Gwamna Bauchi yace ya rubuta wasika zuwa jam'iyyar PDP ta ƙasa ne domin sanar da su yunkurin cin amanarsa da ake a jihar
- Bala Muhammed yace sakamakon haka jam'iyyar ta gayyace shi suka tattauna da ɗan takarar shugaban kasa a inuwar PDP, Atiku Abubakar
- Kwana ɗaya bayan haka aka hangi gwamna Wike ya ja tawagarsa sun kai ziyara ga takwaransu na Bauchi
Bauchi - Gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammed, yace ya rubuta wasika zuwa ga uwar jam'iyyar PDP ta ƙasa domin ya ankarar da kokarin da ake na yi wa kudirin tazarcensa zagon ƙasa a jihar.
Gwamnan ya yi wannan ƙarin haske ne bayan ganawar sirri da gwamnoni biyar na 'Tawagar Gaskiya a PDP' waɗanda aka fi sani da G5 ranar Laraba a jihar Bauchi.
Premium Times ta tattaro cewa Muhammed ya yi tattaunawar sirri da gwamna Nyesom Wike na Ribas, Samuel Ortom na Benuwai, Okezie Ikpeazu na Abiya da kuma Ifeanyi Ugwuanyi na jihar Enugu.
"A matsayin mamba mai biyayya ga jam'iyya na gano ana cin amanata, shiyasa na rubuta wasikar domin jawo hankali," inji Kauran Bauchi.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Meyasa gwamnan ya ziyarci Atiku a Abuja?
Mista Muhammed yace wasikar na ƙunshe tsantsar gaskiya, babu ɓoye-ɓoye kuma cikin aminci, "Wannan ne dalilin da yasa jam'iyya ta gayyace ni mu zauna da ɗan takarar shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar a Abuja."
"Mun yi doguwar tattaunawa zuciya buɗe kuma na sami wasu karin bayanai saboda ba ni kaɗai na aika takardar ba, baki ɗaya iyalan PDP a Bauchi ne suka rubuta da gwamnatin jiha, shiyasa ma naje wurin."
A shirye muke a sasanta - Wike
Da yake nasa jawabin, gwamna Wike jagoran G5 yace kofarsu a buɗe take domin zaman tattaunawa kuma ba su taɓa hana lalubo hanyar samun maslaha ba.
Punch ta ruwaito Wike na cewa:
"Abinda muke cewa kawai shi ne a yiwa kowa adalci da daidaito kuma hakan ne asalin abinda jam'iyyar PDP ta tsayu a kai. Bamu taba kulle kofa ba kuma ba zamklu rufe ba, kawai munce a gyara kuskuren da akai."
A wani labarin kuma Gwamnan Bauchi yace kamata ya yi ace yana cikin tawagr G5 domin yana da alaƙa mai ƙarfi da su
Da yake jawabi a wurin ganawarsu, Gwamna Bala Muhammed, yace tun farko ya dace a ce sun nemi shi amma bisa wani ɓoyayyen dalili basu yi hakan ba.
A kwanan nan, Kauran Bauchi ya shiga kanun labarai biyo bayan wata wasika da ya rubuta dake nuna an masa ba dai-dai ba a jam'iyyar PDP.
Asali: Legit.ng