Mun Ji Dadin Yadda Masu Kokari Irin Su Wike da Umahi Ba Su Samu Tikitin Takarar Shugaban Kasa Ba, Kwankwaso

Mun Ji Dadin Yadda Masu Kokari Irin Su Wike da Umahi Ba Su Samu Tikitin Takarar Shugaban Kasa Ba, Kwankwaso

  • Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar NNPP ya bayyana wasu 'yan siyasa da suka zo razana shi a zaben 2023
  • Gwamnonin Kudu, Wike Umahi ne wadanda Kwankwaso yace sun kasance mutane masu kokari a kasar nan
  • An farmaki tagawar dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a jihar Borno yayin da ya je kamfen a jihar

Abakaliki, Ebonyi - Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar NNPP mai alamar kayan marmari, Rabiu Musa Kwankwaso ya ce ya ji dadin yadda Nyesom Wike da Dave Umahi ba su samu tikitin takarar shugaban kasa ba.

Tsohon gwamnan na jihar Kano ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin da yake zantawa da manema labarai a Abakaliki, babban birnin jihar Ebonyi, TheCable ta ruwaito.

Wike, gwamnan jihar Ribas, mamban jam'iyyar PDP ne kuma ya rasa tikitin takarar shugaban kasa, inda aka ba Atiku Abubakar tutar PDP a zaben 2023.

Kara karanta wannan

PDP ta tona sirri, ta fadi dalilin da yasa 'yan APC suka farmaki tawagar Atiku a Borno

Kwankwaso ya ce Tinubu da Tinubu ba za su tabuka komai ba a 2023
Mun Ji Dadin Yadda Masu Kokari Irin Su Wike da Umahi Ba Su Samu Tikitin Takarar Shugaban Kasa Ba, Kwankwaso | Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Shi kuwa Umahi, dan APC ne kuma ya tsaya takarar shugaban kasa, amma ya rasa tikiti a zaben fidda gwani, aka ba Bola Ahmad Tinubu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Zam lallasa PDP da APC a zabe mai zuwa, mun hango nasara, inji Kwankwaso

Da yake tsokaci a kai, Kwankwaso ya ce zabin 'yan takara da jam'iyyun PDP da APC suka yi ya ba NNPP kwarin gwiwar hango nasara a zaben 2023 mai zuwa, NaijaNews ta tattaro.

A kalamansa:

"Tabbas, zan yi farin cikin mutane kamar Dave a nan, mutane kamar abokina Wike, da wasu da dama, zan yi farin ciki sosai dasu [a matsayin 'yan takarar shugaban kasa].
"Amma ba za mu so su a matsayin abokan hamayya ba, saboda mun san wadannan mutane ne da suka yi aiki tukutu.
"Kun sani sarai abokin hamayya ya kasance laku-laku wanda za a buge da wuri a yi nasara ya fi. Wannan yasa yanzu muke farin ciki, kuma muke samun natsuwa a matakin kasa."

Kara karanta wannan

2023: Kwankwaso Ya Faɗi Sunayen Mutum Biyu Da Yake So Su Zama Shugaban Kasa

PDP ta tafi kamfen Borno, an farmaki tawagar dan takarar shugaban kasa

Jam'iyyun siyasa na ci gaba da gangamin kamfen a fadin kasar nan, a ranar Labara Atiku Abubakar na PDP ya ziyarci jihar Borno don tallata hajarsa.

An samu tsaiko lokacin da wasu tsagerun 'yan daba suka farmaki ayaron motocin tawagar da ya tafi da ita jihar ta Borno.

An daura alhakin farmakin ga jam'iyyar APC mai mulki a jihar Borno.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.