Rikicin PDP: "Abin Da Yasa Ni, Ortom Da Wasu Muka Ziyarci Gwamnan Bauchi", Wike

Rikicin PDP: "Abin Da Yasa Ni, Ortom Da Wasu Muka Ziyarci Gwamnan Bauchi", Wike

  • An bayyana abin da ya kai Gwamna Nyesom Wike da tawagarsa na gwamnonin G5 zuwa jihar Bauchi
  • Wike a ranar Laraba, 9 g watan Nuwamba, ya ce shi da takwarorinsa na PDP sun taho ne don nuna goyon baya ga Gwamna Bala Mohammed
  • Gwamnan na jihar Ribas ya ce sun kuma zo don warware kallubalen da tazarcen Mohammed ke fuskanta

Jihar Bauchi - Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya yi bayanin dalilin da yasa wasu takwarorinsa na jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, suka ziyarci Bauchi.

A gidan gwamnatin Bauchi a ranar Laraba, 9 ga watan Nuwamba, ya ce sun kai ziyarar ne don nuna goyon baya da tarayya ga Gwamna Bala Mohammed, Channels TV ta rahoto.

Gwamna Wike
Rikicin PDP: "Abin Da Yasa Ni, Ortom Da Wasu Muka Ziyarci Gwamnan Bauchi", Wike. Hoto: @GovWike
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

Ana nan tare: Gwamnan PDP Ya Karyata Rade-Radin Watsi da Tafiyar Atiku Abubakar

Wike ya kuma bayyana cewa shi da Gwamna Samuel Ortom, Okezie Ikpeazu da Ifeanyi Ugwuanyi sun taho ne don tattauna abin da za su iya taimakawa da shi don tazarcen Bala, rahoton Premium Times.

A bangarensa, gwamnan na jihar Bauchi ya mika godiyarsa ga takwarorinsa na PDP saboda nuna damuwarsu, ya kara da cewa zai iya bayyanawa bangaren Wike abubuwan da ke damunsa.

Wike, Ortom da Wasu Abokansu Sun Dira Bauchi Domin Jawo Gwamna Tsaginsu

Gwamnonin PDP na G5 da suka yi kaurin suna wurin adawa da tafiyar Atiku, sun dira jihar Bauchi domin kokari janyo gwamna Bala Muhammad na jihar zuwa cikinsu.

The Nation ta rahoto cewa gwamnonin da suka hada da Nyesom Wike na jihar Ribas, Samuel Ortom na jihar Benue, Okezie Ikpeazu na jihar Abia da Ifeanyi Ugwuanyi na jihar Enugu.

Rahotanni sun bayyana cewa, tawagar G5 na kokarin kambama wutar rikici ce da ta barke tsakanin dan takarar shugaban kasa na PDP Atiku Abubakar da gwamna Bala na jihar Bauchi.

Kara karanta wannan

"Kamata Ya Yi Ace Muna Tare": Abinda Gwamnan Bauchi Ya Faɗa Wa Wike da 'Yan G5

Atiku Yana Da Tambayoyi Da Zai Amsa Kan Alakarsa Da Yan Ta'adda, In Ji Fani-Kayode

A bangare guda, jigon APC Femi Fani-Kayode ya alakanta dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar da ta'addanci yana mai cewa akwai bukatar a bincike shi.

Tsohon ministan sufurin jiragen saman ya bayyana hakan ne cikin wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Talata 8 ga watan Nuwamba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164