'Karya Ne' Jam'iyyar APC Ta Maida Kakkausan Martani Kan Zargin Kaiwa Atiku Hari a Borno

'Karya Ne' Jam'iyyar APC Ta Maida Kakkausan Martani Kan Zargin Kaiwa Atiku Hari a Borno

  • Jam'iyyar APC mai mulkin jihar Borno ta karyata labarin dake yawo cewa 'Yan daba sun farmaki Ayarin Atiku a Maiduguri
  • Ali Bukar Dalori, shugaban APC na jiha, yace Dino Melaye karya ya tafka domin babu harkar dabancin siyasa a Borno
  • Kakakin kamfen Atiku ya yi ikirarin cewa aƙalla mutane 74 ke kwance a Asibiti sanadin harin 'yan daban

Borno - Jam'iyyar APC ta nusanta rahoton cewa wasu 'yan daba sun farmaki ayarin ɗan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar, a Maiduguri, jihar Borno ranar Laraba.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa kakakin kwamitin yaƙin Atiku, Sanata Dino Melaye, ya yi ikirarin cewa an kai wa Atiku hari yayin gangamin PDP a jihar Borno.

Jam'iyyar APC mai mulki.
'Karya Ne' Jam'iyyar APC Ta Maida Kakkausan Martani Kan Zargin Kaiwa Atiku Hari a Borno Hoto: vanguardngr
Asali: UGC

Melaye ya ƙara da cewa akalla mutane 74 ke kwance a Asibiti sakamakon harin yayin da maharan suka yi kaca-kaca da Motoci sama da 100.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Jam’iyyar PDP ta Bayyana Shirinta Na Hambarar Da APC A Wani Babban Jihar Arewa

Sanatan ya zargi APC da ɗaukar nauyin harin inda yace jam'iyya mai mulki na kokarin dakatar da kamfem ɗin da suka zo yi a jihar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

APC ta maida kakkausan raddi ga Melaye

Da yake martani, shugaban APC na jihar Borno, Ali Bukar Dalori, yace sam babu inda Yan Daban APC suka kai hari kan wani Ayarin jam'iyyar hamayya a faɗin jihar.

Dalori ya shaida wa jaridar cewa Sanata Melaye ƙarya ya kwararo, "Na ji takaicin zargin da Dino Melayi ya yi cewa 'yan Daban APC ne suka farmaki Ayarin Atiku Abubakar yayin da ya zo kamfe Maiduguri."

"Kowa ya san cewa tun lokacin da gwamna Babagana Umaru Zulum ya karɓi mulki ya haramta dabar siyasa a baki ɗaya sassan jihar nan. Jam'iyyarmu mai albarka tana bin doka sau da ƙafa."

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: 'Yan ta'adda sun farmaki tawagar dan takarar shugaban kasan APC a Borno

"Kuma mu da muke da gwamnati bamu hana jam'iyyar PDP wurin da zata gudanar da taronta ba kamar yadda muke gani a wasu jihohin. Abinda na sani kawai babu ɓurbushin PDP a Borno."

Ba zamu shiga zaben Neja ba - PDP

A wani labarin kuma jam'iyyar PDP tace ba ta yarda da shirin hukumar zaɓe ta jihar Neja na gudanar da zaɓen kananan hukumomi gobe ba

A wata sanarwa da ta fitar, PDP mai adawa a jihar tace ba zata wahal da kanta ta shiga zaɓen ba kuma yaɓzu haka ta kai ƙara Kotu.

A gobe Alhamis, 10 ga watan Nuwamba, 2022, hukumar zaɓe ta jiha ta shirya gudanar da zaɓe a sassan kananan hukumomin jihar 25.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262