Awanni Gabanin Farawa, PDP Ta Tsame Kanta Daga Zaɓen Kananan Hukumomin Neja

Awanni Gabanin Farawa, PDP Ta Tsame Kanta Daga Zaɓen Kananan Hukumomin Neja

  • Jam'iyyar adawa PDP ta sanar da cewa ba zata shiga fafafatawa a zaɓen kananan hukumomin jihar Neja ba
  • Shugaban PDP reshen jihar, Barista Tanko Beji, yace sun kai ƙara gaban Kotu domin hukumar zaɓe ta saba wa dokoki
  • Gwamnatin Neja karkashin gwamna Sani Bello, ta ba da hutun kwana guda domin kowa ya samu damar sauke hakkin zaɓe

Niger - Jam'iyyar PDP reshen jihar Neja tace ba zata shiga zaɓen kananan hukumomin da aka shirya gudanarwa gobe Alhamis ba a jihar.

Shugaban PDP na jiha, Barista Tanko Beji, yace hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Neja ta saɓa wa dokoki da ƙa'idojin gudanar zaɓen.

Babbar jam'iyyar adawa, PDP.
Awanni Gabanin Farawa, PDP Ta Tsame Kanta Daga Zaɓen Kananan Hukumomin Neja Hoto: dailytrust
Asali: UGC

A wata sanarwa da ya fitar, Barista Beji yace tuni jam'iyyar PDP ta shigar da ƙara gaban Kotu domin haramtawa hukumar (NSINEC) ci gaba da shirye-shiryen gudanar zaɓen kamar yadda ta tsara.

Kara karanta wannan

Sabbin Rigingimu Sun Kara Ɓarkewa a Jam'iyyar PDP Kan Kuɗin Yakin Neman Zaben Atiku 2023

Shugaban PDP na jihar yace har yanzun batun na gaban Kotu ba'a gama ƙarƙarewa ba, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Beji ya koka kan cewa ba kowane mai haƙƙin kaɗa kuri'a bane hukumomi masu alhaki suka baiwa katin zaɓe na dindindin (PVC)

A cewarsa, ci gaba da tafiya kan yadda aka tsara na gudanar da zaɓe gobe Alhamis, 10 ga watan Nuwamba, 2022 zai tauye wa da yawan mutane hakkinsu na zaɓe.

Gwamnatin Neja ta ba da hukun kwana ɗaya

Jaridar Punch tace gwamnan jihar Neja, Muhamad Sani Bello, ya ayyana gobe Alhamis, 10 ga wata a matsayin ranar hutu domin gudanar da zaɓe a kananan hukumomi 25 dake sassan jihar.

Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwa da Sakataren gwamnatin jihar, Ahmed Matane, ya fitar a Minna, babban birnin Neja.

Kara karanta wannan

2023: Jam'iyyar APC Ta Samu Gagarumin Goyon Baya, Jiga-Jigan PDP Sama da 300 Sun Koma Bayan Tinubu

Yace hutun zai baiwa kowane mazauni cikakken damar da zai garzaya runfar zaɓensa ya kaɗa kuri'a ga wanda yake so ya jagorancesu.

A wani labarin kuma babban jigon APC a jihar Kuros Riba, Sam Bassey, yace yana nan daram a jam'iyya mai mulki amma ɗan takarar PDP zai wa aiki a 2023

Mista Bassey ya bayyana haka ne jim kaɗan bayan wani taron da masu ruwa da tsaki da suka gudanar da garin Biase, kusa da babban birnin jihar.

A cewar tsarin da APC mai mulki ta ɓullo da shi wani yunkuri ne na tauye kananan mazaɓu da hanasu hakkkin tsayawa takara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel