Wasu Tsageru Sun Farmaki Tawagar Atiku a Jihar Borno, an Ji Harbe-Harbe
- Wasu da ake zargin 'yan daban siyasa ne sun farmaki tawagar kamfen dan takarar shugaban kasan PDP, Alhaji Atiku Abubakar
- Majiya ta shaida cewa, akalla mutane 70 ne suka samu raunuka daga tawagar Atiku, kuma yanzu haka suna can asibiti
- Kakakin kamfen PDP ya daura alhakin wannan mummunan hare da ya yi sanadiyyar lalacewar motoci kan jam'iyyar APC mai mulkin Borno
Jihar Borno - An farmaki tawagar kamfen dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar a birnin Maiduguri na jihar Borno a ranar Laraba 9 ga watan Nuwamba.
Wani bidiyo da aka yada a kafar sada zumunta ya nuna lokacin da jama'a ke gudun tsire daidai sadda ake jin harbe-harben bindiga a wurin.
Tawagar kamfen ta PDP dai ta dura jihar ne don fara gangaminta na kamfen a jihar da take karkashin inuwar jam'iyyar APC a Arewa maso Gabas.
Wakilin Daily Trust ya ce ya ga motcin da aka lalata daga tawagar Atiku a Ramat Square da babban birnin jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Yan APC ne suka farmaki tawagar kamfen din mu, inji kakakin PDP
Kakakin tawagar kamfen din, Sanata Dino Melaye ya daura alhakin harin kan jam'iyyar APC ta jihar Borno.
Melaye ya koka da cewa, akalla mutane 70 ne suka samu raunuka daga wannan mummunan harin.
Ya ce:
"Suna so ne su hana mu gudanar gangamin kamfen, da nake magana yanzu, mutum 74 sun samu raunuka an kwantar dasu a asibiti.
"'Yan daban APC sun lalata motoci da dama."
Rahoton jaridar Vanguard ta bayyana cewa, akalla motoci 100 ne suka lalace a wannan harin da aka kai.
Majiya ta ce ta ga 'yan daban siyasa da dama a wurare daban-daban a kan titin Maiduguri zuwa Kano.
Gwamnonin G-5 masu adawa da Atiku sun kai ziyara jihar Bauchi
A gefe guda, yayin da gangamin kamfen dan takarar shugaban kasa na PDP ya karkata zuwa jihar Borno, gwamnonin G-5 sun taru a jihar Bauchi don wata ganawa.
Gwamnoni hudu ne suka halarci zaman, wanda gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad ya zama mai masaukin baki a jiharsa.
PDP na fuskantar rikici, tun bayan da gwamnonin G-5 suka fara bayyana bukatar tsige shugaban jam'iyya Iyochia Ayu.
Asali: Legit.ng