Gwamnan PDP Ya Ɗau Zafi, Yace Gara Ya Mutu Da Ya Gogi Bayan Atiku a 2023

Gwamnan PDP Ya Ɗau Zafi, Yace Gara Ya Mutu Da Ya Gogi Bayan Atiku a 2023

  • Gwamnan jihar Benuwai, Samuel Ortom, yace ba zai mara wa ɗan takarar PDP, Atiku Abubakar baya ba a 2023
  • Gwamnan, wanda ya fito daga arewacin Najeriya yace ya gwammaci ya mutu da ya goyi bayan Bafullatani ya zama shugaban ƙasa
  • Ortom na ɗaya daga cikin tawagar gwamnoni 5 da suka ware kansu a PDP kuma suka nemi Ayu ya yi murabus

Benue - Gwamnan Jihar Benuwai, Samuel Ortom, ya aike da kakkausan sako ga Atiku Abubakar, mai neman shugaban kasa a inuwar PDP, ya faɗa masa ba zai goyi bayan takararsa ba.

Jarisar The Nation ta rahoto Gwamnna Ortom na faɗa wa Atiku cewa can ta matse masa, amma ba zai mara masa baya ba yayin da Fulani ke kashe mutanensa a Benuwai.

Gwamna Ortom da Atiku.
Gwamnan PDP Ya Ɗau Zafi, Yace Gara Ya Mutu Da Ya Gogi Bayan Atiku a 2023 Hoto: thenation
Asali: UGC

Ortom ya yi wannan furucin ne ranar Lahadi da daddare yayin da ya karɓi bakuncin gwamnonin G-5 da suka haɗa da, Nyesom Wike na Ribas, Okezie Ikpeazu na Abiya; Seyi Makinde na Oyo da Ifeanyi Ugwuanyi na Enugu.

Kara karanta wannan

2023: Bayanai Sun Fito, Abinda Gwamnan Bauchi Ya Faɗa Wa Ortom Kan Kalaman Fulani da Atiku

Gwamnan ya koka da kisan da aka yi wa mutane 18 a ƙaramar hukumar da ya hito a makon da ya gabata, inda yace:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Can ta matse wa Atiku da duk masu goyon bayansa, ku je ku gaya masa shin yana son na zama bawan Fulani ne? Gara na mutu, duk mai ƙaunar Atiku maƙiyin jihar Benuwai ne."
"Ana ta kashe mutane na amma ku ce in yi shiru. Wa'adin mulkina zai kare a watan Mayu, daga nan zaku iya mun duk abinda kuka ga dama idan kuna tunanin kuna da mulki, na riga na rubuta wasiyyata."
"Lokacin da na baiwa matata wasiyyata, shafe dare ta yi tana kuka. Idan na mutu a 62 da yawan sa'annina sun riga ni tafiya. Idan yanzun na mutu na cimma nasara amma kowa ya sani na mutu ne a kokarin kare rayuwar mutane na."

Kara karanta wannan

Ana nan tare: Gwamnan PDP Ya Karyata Rade-Radin Watsi da Tafiyar Atiku Abubakar

- Samuel Ortom.

Ba zan taba goyon bayan Bafullatani ya zama shugaban kasa ba - Ortom

Bugu da ƙari, Gwamna Ortom yace ba zai taɓa tallafa wa Fulani ya ɗare kujerar shugaban ƙasa ba a Najeriya ba.

"Ba zan taɓa goyon bayan Bafullatani ya zama shugaban ƙasa ba, idan akwai wani mutum da ke bukatar aiki da ni kuma ya tabbatar da tsare rayukan mutanena, na shirya aiki da shi."

A wani labarin kuma Gwamna Wike Ya Jagoranci Tawagar Gwamnonin PDP 5 Sun Dira Benuwai

Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya jagoranci takwarorinsa na G-5 zuwa jihar Benuwai dake arewacin Najeriya.

Wasu hotuna da suka bayyana sun nuna yadda gwamna Samuel Ortom ya tarbe su hannu bibbiyu cikin farin ciki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel