Zaben 2023: Aikin Atiku Shine Haɗa Kan Najeriya Ba PDP Ba, In Ji Anenih
- Ose Anenih, mamba a kwamitin yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa ya ce aikin Atiku Abubakar shine hada kan Najeriya
- Dan tsohon jigon PDPn, Tony Anenih, ya ce aikin shugaban jam'iyya na kasa da NWC ne su hada kan jam'iyya ba dan takarar shugaban kasa ba
- Anenih ya yi wannan furucin ne a matsayin martani ga kalaman Kashim Shettima, dan takarar mataimakin shugaban kasa na APC, inda ya gorantawa Atiku kan rashin iya hada kan jam'iyya
Mamban kwamitin yakin neman zabe shugaban kasa na Atiku Abubakar, Ose Anenih, ya ce aikin dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar ta Peoples Democratic Party, PDP, shine hada kan Najeriya, ba jam'iyya ba.
Ose Anenih ya bayyana hakan ne yayin hira da shi da aka yi a shirin Politics Today na Channels Television, Daily Trust ta rahoto.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Hada kan jam'iyya aikin shugaban jam'iyya ne da NWC, Anenih
Dan marigayin jigon PDP, Cif Tony Anenih, ya ce dauyin hada kan jam'iyya ya rataya ne kan shugaban jam'iyyar na kasa da kwamitin gudanarwa na kasa, NWC.
Ya furta hakan ne a matsayin martani kan kalaman dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar APC, Kashim Shettima, lokacin da ya ce idan dan takarar shugaban kasa na PDP ya gaza hada kan jam'iyya ya zai hada kan kasa, rahoton Head Topics.
Kalamansa:
"Dan takara na (Atiku) shine dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP; aikinsa shine hada kan Najeriya da ke takarar shugabanta. Muna da shugaban jam'iyya na kasa da NWC da ke kula da harkokin yau da gobe na jam'iyya da warware duk wata matsala da ta taso a jam'iyyar.
Rikicin PDP: Za A Cire Iyorchia Ayu? Atiku Ya Bayyana Matakinsa Na Ƙarshe, Ya Aika Sako Ga Wike Da Saura
"Ba maganan dan takara na bane, batu ne na cewa dan takara na zai hada kan Najeriya."
Abin Da Wike Ya Fada Wa Atiku A Sabuwar Ganawar Da Suka Yi Kan Rikicin PDP
A kokarin warware rikicin jam'iyyar PDP, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya sake ganawa da Gwamna Mr Nyesom Wike na Jihar Rivers.
Wata majiya da ta halarci taron ta shaidawa Daily Trust cewa wasu hadiminan bangarorin biyu sun halarci taron.
An yi ganawar ne a gidan gwamnatin Rivers da ke Asokoro a Abuja a ranar Alhamis.
Asali: Legit.ng