Zaben 2023: Labour Party Na Tattaunawa Da Kwankwaso Har Yanzu, In Ji Okupe

Zaben 2023: Labour Party Na Tattaunawa Da Kwankwaso Har Yanzu, In Ji Okupe

  • Akwai yiwuwar jam'iyyun hamayya su hada kai kafin babban zaben shekarar 2023 da ke tafe
  • Direkta Janar na kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party, Dr Doyin Okupe ya sanar da hakan
  • Jigon jam'iyyar ya ce har yanzu suna tattaunawa da wasu jam'iyyun ciki har da NNPP da SDP

FCT, Abuja - Shugaban kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party, LP, Dr Doyin Okupe ya ce jam'iyyarsu har yanzu tana tattaunawa da dan takarar shugaban kasa na NNPP, Rabiu Kwankwaso da wasu da nufin hadin gwiwa gabanin zaben 2023.

A farkon wannan shekarar, akwai rahotannin cewa Kwankwaso da Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na LP, na tattaunawa kan yiwuwar hada kai, amma bai yiwu ba.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Za A Cire Iyorchia Ayu? Atiku Ya Bayyana Matakinsa Na Ƙarshe, Ya Aika Sako Ga Wike Da Saura

Peter Obi
Zaben 2023: Labour Party Na Tattaunawa Da Kwankwaso Har Yanzu, In Ji Okupe. Hoto: @PeterObi
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Okupe, tsohon mai magana da yawun shugaban kasa, amma, ya ce LP na duba yiwuwar hada kai da Kwankwaso da wasu jam'iyyun.

Ya fada wa Channels Television cewa:

"A matsayin mu na jam'iyya, a matakin kamfen, muna magana da SDP; muna magana da Kwankwaso da tawagarsa. Muna magana da PRP da ADC.
"Na yi imanin Allah zai taimake mu daga yanzu zuwa Disamba, za mu kawo wani gamayyar siyasa a kasar da zai zama alheri.
"Duk wanda ya ci nasara ba kawai yana cin nasara ne da kokarin mutum daya ba; za mu yi nasara ne tare da hadin kan kungiyoyi da dama."

Ba laifi bane don Obi ya ziyarci wadanda ba su goyon bayansa, ba makiyan mu bane - Okupe

Ya kuma yi watsi da suka kan ziyarar da Obi ya kai wa wasu manya a kasar, yana mai cewa an yi hakan ne kawai don a tafi tare da kowa, Daily Post ta rahoto.

Kara karanta wannan

2023: Nasarar APC Na Cikin Haɗari, In Ji Shugaban Kamfen Na Adamawa

Ya ce:

"Wane ya ci zabe a kasarnan, bai yi mulki ba. Yan Najeriya da dama na sonsa amma wasu masu ruwa da tsaki suka tsayar da hakan. Ya kamata mu gujewa hakan ta hanyar janyo kowa a jiki.
"Ko da ba su yarda da mu da farko ba, mu cigaba da adawa da mu; kada su mana kallon makiya. Mu ba makiyan kowa bane, ko wata kungiya ko sashin kasar nan. Kawai mu mutane ne da ke nufin kasar nan da alheri."

Zaben 2023: Peter Obi Ya Ce Ko Ƴaƴan Cikinsa Ba Su Yarda Da Shi Idan Ya Yi Alƙawari, Mutane Sun Yi Martani

Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party, LP, yana shan suka a soshiyal midiya saboda amsar da ya bada kan tambayar da aka masa game da yadda zai farfado da lantarki a Najeriya.

Mai gabatar da shirye-shirye a gidan talabijin na Arise TV ya ce wannan shine dalilin da yasa ya kamata dan takarar LP din ya fitar da manufofinsa ga kasar a rubuce don mutane su gani su yi nazari.

Kara karanta wannan

APC ta tono irin rikicin da PDP ke ciki, ta ce ba za ta tabuka komai a zaben 2023 ba

Asali: Legit.ng

Online view pixel