Akwai Matsala: Jigo Ya Gargadi Jam’iyya, Yace ‘Dan Takaran Kano Yana Tare da Atiku
- Alhassan Ado-Doguwa ya zargi shugabannin APC na jihar Kano da yin watsi da wasu ‘yan jam’iyya
- Ganin halin da abubuwa suke tafiya, Alhassan Ado-Doguwa yana tsoron Rabiu Kwankwaso a 2023
- ‘Dan majalisar yace Murtala Sule Garo yana goyon bayan Atiku Abubakar a kan ‘dan takaran APC
Kano - Alhassan Ado-Doguwa ya ankarar da jam’iyyarsa ta APC a game da rikicin cikin gidan da ake fama da ita a jihar Kano, yace za a iya rasa zabe.
Premium Times tace Hon. Alhassan Ado-Doguwa ya kira taron manema labarai a ranar Juma’a, inda ya koka a kan yadda abubuwa suke tafiya a Kano.
Shugaban masu rinjaye na majalisar tarayyan yace Gwamna Abdullahi Ganduje ya yi kokari a mulki, amma ya bar APC a hannun masu neman kashe ta.
Ado Doguwa ya shaidawa manema labarai cewa bai yarda da Murtala Sule Garo mai neman takarar mataimakin gwamnan jihar Kano a inuwar APC ba.
‘Dan majalisar mai wakiltar mazabar Doguwa/Tudun Wada yana zargin Murtala Sule Garo yana goyon bayan Atiku Abubakar na PDP wanda Surukinsa ne.
A wani bidiyo, Legit.ng Hausa ta saurari ‘dan siyasar yace Murtala Garo ya shaida masa zai fi so PDP ta lashe zaben shugaban kasa saboda alakarsa da Atiku.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Kwankwaso: APC tana ganin barazana - Doguwa
Punch ta rahoto Doguwa yana mai fada, yana kuma kara nanatawa cewa jam’iyyar APC tana cikin babbar matsala a reshen Kano a dalilin rigimar cikin gida.
A cewar ‘dan majalisa, abin ya jawo rigimar shi ne an yi watsi da wasu ‘ya ‘yan jam’iyya, wanda wannan zai sa NNPP ta samu nasara a kan APC a 2023.
A jawabin da ya yi, Doguwa yace za su iya shan kunya a hannun tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Kwankwaso, wanda ya kira gawurtaccen ‘dan siyasa.
Wasu ’yan tsiraru wadanda ba su cancanta ba, su kadai suke gudanar da jagoranccin jam’iyyar APC. Ina batun siyasar Kano ne, jam’iyyarmu ta APC.”
- Alhassan Ado-Doguwa
Sai manya sun tsoma baki a APC
Martala Garo shi ne wanda ya maida ‘yan majalisa saniyar ware a wajen harkokin jam’iyya mai mulki, wannan yana cikin abubuwan da Doguwa ya fada.
An rahoto ‘dan majalisar yana kira ga Mai girma Muhammadu Buhari da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje su shawo kan wannan matsala tun da wuri.
Rikicin PDP a Ribas
Bayan watanni 6 da mallaka masa fili a unguwar GRA, an ji labari Gwamnatin Nyesom Wike ta karbe fulotin wani na hannun daman Atiku Abubakar.
Sanata Lee Maeba shi ne yake jagorantar yi wa Atiku Abubakar kamfe, yayin da Nyesom Wike yake yakar ‘dan takaran shugaban kasar na PDP a Ribas.
Asali: Legit.ng