Bita-da-kulli: Gwamnan Ribas Ya Raba Sanata da Fulotinsa 'Saboda' Yana Tare da Atiku

Bita-da-kulli: Gwamnan Ribas Ya Raba Sanata da Fulotinsa 'Saboda' Yana Tare da Atiku

  • Gwamnatin jihar Ribas ta aikawa Lee Maeba takarda cewa an karbe wani fulotinsa a Fatakwal
  • Sanata Lee Maeba ya rasa filin da ke unguwar GRA ne watanni shida bayan Gwamna ya mallaka masa
  • Tsohon Sanatan shi ne Shugaban kwamitin da ke yakin neman zaben Atiku Abubakar a jihar Ribas

Abuja - Gwamnatin jihar Ribas ta karbe takardar fili watau CoC da aka ba tsohon ‘dan majalisar dattawa, Sanata Lee Maeba a unguwar GRA a Fatawakal.

Punch a rahoton da ta fitar dazu, ta bayyana cewa Sanata Lee Maeba jigo a PDP, shi ne shugaban kwamitin yakin neman zaben Atiku Abubakar a jihar Ribas.

A wata takarda da ma’aikatar filaye da safayo ta aikawa Maeba a ranar Laraba, 2 ga watan Nuwamba, an sanar da shi an karbe filin da aka taba ba shi.

Kara karanta wannan

Tabbatar da tsaro: An kama wasu masu hakar ma'adinai ba bisa kai'da ba a Abuja

Darektar rikon kwarya ta sashen mallakar filaye ta ma’aikatar filaye da safayo, Ochiagha Onyebuchi ta rubuta takardar a madadin babbar sakatare.

“An umarce ni in sanar da kai cewa an karbe filinka da ke kan Plot 20A, Golf Course Layout, tsohuwar GRA, Fatawal kamar yadda wallafar da gwamnatin jihar Ribas mai lamba No. 22 Vol. 58 na 20 ga watan Satumba 2022 ta nuna.
Sakataren din-din-din ya na mai aiko da gaisuwarsa.”

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

- Ochiagha Onyebuchi

Gwamnan Ribas
Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas Hoto: @GovWike
Asali: Twitter

Wata 6 da suka wuce aka ba ni filin

Da aka yi magana da tsohon Sanatan na Kudu maso gabashin Ribas, a fusace ya tabbatar da cewa gwamna ne ya ba shi filin watanni shida da suka wuce.

Tun da aka gudanar da zaben fitar da gwani na ‘dan takarar shugaban kasa, aka samu sabani tsakanin Atiku Abubakar da ya yi nasara da Nyesom Wike.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Daukarwa Al’ummar Kogi Gagarumin Alkawari Gabannin Zaben 2023

Ana zargin gwamna Wike yana neman ganin bayan ‘yan PDP da ke tare da Atiku a Ribas.

Bayan Celestine Omehia ya ziyarci ‘dan takaran shugaban kasa a PDP, sai aka ji cewa majalisar dokokin Ribas ta cire masa matsayin tsohon Gwamnan jihar.

Gwamnati ta bada umarni an rufe gidan man Hon. Chinyere Igwe, wanda yanzu ‘dan majalisar wakilan tarayya ne wanda yake goyon bayan Atiku Abubakar.

Sauran magoya bayan Atiku sun hada da tsohon mataimakin shugaban majalisa, Rt. Hon Austin Opara da Austin Sekibo da aka ji Gwamnan ya taso a gaba.

Peter Obi ya cancanta- Ortom

A jiya aka samu rahoto Samuel Ortom yace ba don shi jam’iyyar PDP ba ne, da ya yi wa Peter Obi da Jam’iyyarsa ta LP aiki a zaben Shugaban kasa na 2023.

Mai girma Ortom yace duk da irin cacantar Peter Obi, iyakarsa da shi a zabe mai zuwa shi ne addu’a domin shi yana neman takara ne a jam'iyyar PDP.

Kara karanta wannan

Rabiu Kwankwaso Ya Zauna da Jakadun Kasashe 25, Ya Bayyana Dalilin Haduwarsu

Asali: Legit.ng

Online view pixel