Sanata Binani Ta Sauka daga Shugabancin Kwamitin Yakin Zaben Tinubu na Adamawa

Sanata Binani Ta Sauka daga Shugabancin Kwamitin Yakin Zaben Tinubu na Adamawa

  • Sanata Aishatu Binani ta sanar da janyewa daga shugabancin ragamar tawagar kamfen din Tinubu da Shettima da aka bata na jihar Adamawa
  • Kamar yadda ta sanar a wata takarda da ta fitar, tace ta janye ne har zuwa lokacin da kotun daukaka kara zata yanke hukunci a kan shari’arta dake gabansu
  • Tayi kira ga PCC ta nada shugaban rikon kwarya saboda ta matukar fusata da abinda shugabannin jam’iyyar ke yi mata a jihar da wasu masu ruwa da tsaki

Adamawa - Sanata Aishatu Binani ta bayyana cewa ta janye daga shugabancin kwamitin yakin neman zaben Tinubu a jihar Adamawa.

Aishatu Binani
Sanata Binani Ta Sauka daga Shugabancin Kwamitin Yakin Zaben Tinubu na Adamawa. Hoto daga channelstv.com/dailytrust.com
Asali: UGC

A takardar da ta saka hannu da kanta a kai, ta bayyana cewa ta sauka ne har zuwa lokacin da kotun daukaka kara zata yanke hukunci kan karar da ta mika ta hana ta takarar kujerar gwamnan jihar a zabe mai zuwa.

Kara karanta wannan

PDP ga Shettima: Cutar Mantau Ke Damunka, Gidanku Yana Ci da Wuta, Ku Fara Magance shi

Wata babbar kotun tarayya ta soke zaben fidda gwani da Aishatu Binani tayi nasarar a jihar.

“Sanata Aishatu Binani ta sauka daga shugabancin tawagar yakin neman zaben Tinubu da Shettima har zuwa lokacin da kotun daukaka kara zata yanke hukunci. Ana kira ga kwamitin da su hanzarta nada shugaban rikon kwarya a cikin kankanin lokaci.”

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

- Takardar tace kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Shugabancin APC na jihar karkashin Samaila Tadawus ya zargi Binani da yin watsi da jam’iyyar tare da zaben tawagar kamfen din ita kadai ba tare da tuntubarsu ba, Daily Nigerian ta rahoto.

Wata majiya kusa da Binani ta sanar da Daily Trust cewa, ta yanke hukuncin sauka daga mukamin a ranar Alhamis bayan ta fusata da kalaman da wani mamban jam’iyyar yayi a kan wasu manyan masu ruwa da tsaki da suka hada da tsohon Gwamnan jihar Murtala Nyako.

Kara karanta wannan

Matashi Ya Gurfana a Kotu Kan Zargin Mazge Matar Aure Har Cikinta Ya Zube

Kotu ta Fatattaki Aishatu Binani Matsayin ‘Yar Takarar Gwamna a APC a Adamawa

A wani labari na daban, wata babbar kotun tarayya dake zama a Yola ta soke zaben fidda gwani na kujerar Gwamnan APC na jihar Adamawa wanda ya samar da Aishatu Binani matsayin ‘yar takarar kujerar Gwamnan jihar a jam’iyyar, Channels TV ta rahoto.

Kotun a ranar Juma’a ta bayyana cewa jam’iyyar APC bata da ‘dan takarar kujerar Gwamna a jihar a zaben 2023 mai gabatowa amma tace daga mai kara har wanda aka yi kara suna da damar daukaka kara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel