Akwai Yuwuwar ’Yan Siyasa Su Yi Amfani Da ’Yan Daba Wajen Gangamin Kamfen Zaben 2023, Inji DSS
- Daraktan hukumar DSS ya bayyana cewa, akwai yiwuwar 'yan siyasa su yi amfani da tsageru a zaben bana
- Ya bayyan bukatar a hada kai wajen tabbatar da an shawo kan matsalolin da suka shafi tsaro a jihohin kasar nan
- Jihohin Arewa maso Yamma na fuskantar hare-haren 'yan bindiga a yankuna daban-daban a shekarun nan
Kaduna - Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta gargadin cewa, akwai yiwuwar 'yan siyasa a kasar nan su yi amfani da tsagerun 'yan daba a gangamin su na zaben 2023, Daily Trust ta ruwaito.
Wannan na fitowa ne daga bakin daraktan DSS a Kaduna, Mr Abdul Enachie yayin gabatar da rahotonsa kan tsaro a jihar ta Kaduna.
Ya bayyana cewa, akwai bukatar gwamnati ta mai da hankali sosai tare da wayar da kan matasa don gudun amfani dasu wajen aikata barna a fadin kasar nan.
A baya hukumar DSS ta gargadi 'yan siyasa da su guji amfani da 'yan daba wajen tarukan gangamin kamfen din zabe mai zuwa, rahoton This Day.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Jama'a su hada kai da jami'an tsaro
Ya kuma bukaci jama'ar gari da su taimakawa hukumomin tsaro wajen gano wanda ke kai bayanai ga 'yan bindiga da sauran ta'adda a jihar da sauran yankunan kasar nan.
Ya shaida cewa, gane masu kai wa 'yan bindiga bayanai ba aikin jami'an tsaro bane kadai, inda ya ce nauyi ne da ya rataya a wuyan duk wani dan kasa nagari.
A bangare guda, ya bukaci sojoji da su fadada ayyukansu na kakkabe maboyun 'yan ta'adda zuwa yankunan Birnin Gwari da kewaye don zakulowa da fatattakar 'yan bindiga.
Da yake kira ga gwamnatin tarayya, ya ce akwai bukatar kammala aikin babban titin Kaduna zuwa Abuja da kuma ta Birnin Gwari, yace hakan zai taimaka wajen inganta tsaron yankunan.
A nasa jawabin, gwamna El-Rufai ya bukaci hukumomin tsaro da su tabbatar da cewa, dukkan 'yan siyasar da ke aiki da 'yan daba an gano su kuma an hukunta su daidai da tsarin doka kafin zaben na 2023.
Sojoji Sun Kama Mutum 60 da Ke Hakar Ma’adinai Ba Bisa Ka’ida Ba a Abuja
A wani labarin, a kokarin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a babban birnin tarayya Abuja, jami’an sojin Najeriya sun kai samame wani yankin hakar ma’adinai da ake haka ba bisa ka’ida ba.
An kai farmakin ne a yankin Tukashara Wasa, Apo a tsakiyar birnin tarayya Abuja, Daily Trust ta ruwaito.
Wannan batu na zuwa ne ta bakin Manjo Janar Musa Danmadami, babban daraktan yada labarai na gidan tsaro a Najeriya.
Asali: Legit.ng