Shugabar Matan PDP Ta Zamfara Madina Shehu Ta Koma APC Mai Mulki

Shugabar Matan PDP Ta Zamfara Madina Shehu Ta Koma APC Mai Mulki

  • Shugabar mata ta PDP ta bayyana sauya sheka zuwa APC saboda rashin shugabanci nagari da jam'iyyar ke fuskanta
  • Gwamnan jihar Zamfara ya karbi shugabar mata ta jam'iyyar PDP a jiharsa zuwa jam'iyyarsu ta APC
  • Matawalle ya raba motoci ga wata tawagar kamfen dinsa, inda ya bayyana wadanda za su amfana da motocin

Gusau, jihar Zamfara- Madina Shehu, shugabar mata ta jam'iyyar PDP a jihar Zamfara ta bayyana sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulki a jihar.

Madina ta bayyana sauya shekarta ne a ranar Alhamis 3 ga watan Nuwamba a birnin Gusau bayan ganawa da gwamna Mawatalle na jihar Zamfara.

Ta bayyana dalilin komawarta APC da cewa, sam babu shugabanci nagari a jam'iyyar PDP, kamar yadda TheCable ta ruwaito.

Shugabar mata a PDP ta sauya sheka zuwa APC
Shugabar Matan PDP Na Zamfara Madina Shehu Ta Koma APC Mai Mulki | Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

A kalamanta:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

2023: Jerin Makusantan Amaechi Da Suka Fice Daga APC Suka Koma Wurin Wike A PDP Ta Jihar Ribas

"Na ayyana sauya sheka zuwa APC tare da shugabannin mata na kananan hukumomi 14 na jihar."

Matawalle ya yi musu kyakkyawar tarba

Da yake marabtarta zuwa APC, gwamna Matawalle ya bayyana wannan mataki da ta dauka na shiga APC a matsayin abin da ya dace kuma ci gaba ga APC.

A cewarsa:

"Karin wadanda suka sauya sheka suna zuwa APC daga PDP. Nan kusa, za mu karbi mambobin PDP ciki harda shugabanninsu."

Gwamna Matawalle ya yi rabon motoci ga tawagar jam'iyyar APC

A wani ci gaban a ranar Alhamis, gwamna Matawakke ya sanar da ba da motoci 17 ga tawagar gangami ta 'Matawalle/Shehi Amalgamated Mobilisation Group' da ke aikin kamfen sake dawowar Matawalle gwamna.

Da yake jawabi yayin ba da motocin, ya ce:

"An ba da motoci bas biyu ga shugabannin tagawar yayin da aka ba da daya kuma ga fannin mata na tagawar.
"Peugeot 406 Wagon guda 14 kuma an ba da su ne ga masu gudanarwa na tawagar a kananan hukumomi 14 na jihar."

Kara karanta wannan

Yanzu: Shugaban PDP na wata jiha a Arewa ya yanki jiki ya fadi matacce ana tsaka da taro

Gwamnan na Zamfara ya kuma bukaci mambobin jam'iyyar da su hada kai don tabbatar da nasarar APC a zabukan da za su gudana a 2023.

Hakazalika, ya bayyana alkawarin ci gaba da ba tawagar gudunmawa don tabbatar da an haifar da mai ido a zabe mai zuwa, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

PDP a dabaibaye take da kitimurmura, ba ta da mafita nan da zabe mai zuwa, inji APC

A wani labarin, Felix Morka, kakakin jam'iyyar APC ya bayyana irin halin matsi da rikici da jam'iyyar adawa ta PDP ke ciki a halin yanzu, The Cable ta ruwaito.

Ya bayyana hasashensa game da makomar PDP a yayin tattaunawa da gidan talabijin na Legas a ranar Laraba, inda yace ba zai yiwu PDP ta warware damuwar da take ciki ba nan da zaben 2023.

Idan baku manta ba, PDP ta tsunduma cakwalkwalin rikici ne tun a watan Mayu, lokacin da Atiku Abubakar ya zama dan takarar ta na shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Shirin 2023: Atiku ya samu nakasu a Sokoto, manyan jiga-jigai sun koma APC

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.