Ambaliyar Ruwa: Matasan Neja Delta Sun Cimma Matsayi Mai Muhimmanci, Sun Tura Wa Buhari Saƙo

Ambaliyar Ruwa: Matasan Neja Delta Sun Cimma Matsayi Mai Muhimmanci, Sun Tura Wa Buhari Saƙo

  • An yaba wa gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari kan kokarinsa na rage radadin mutanen da ambaliyar ruwa ya shafa
  • Shugaban kungiyar matasan yankin Neja Delta wanda shima ambaliyar ya shafe shi ne ya yi wannan yabon ga shugaban kasa
  • A cewar matasan, shugaban kasar ta hannun Hukumar bada agajin gaggawa, SEMA, na cigaba da bada kayayakin tallafi ga mutanen yankunan da ambaliyar ya shafa

Neja-Delta - Ambaliyar ruwa da ya faru a baya-bayan nan ya jefa mutane da dama cikin damuwa ko rasa muhallinsu, Daily Trust ta rahoto.

Da hakan ne matasa daga yankin Neja Delta sun yaba wa Shugaba Muhammadu Buhari da Hukumar Bada Agajin Gaggawa, NEMA, saboda tallafi daban-daban da aka kaiwa mutanen yankin.

Buhari signs
Ambaliyar Ruwa: Matasan Neja Delta Sun Cimma Matsayi Mai Muhimmanci, Sun Tura Wa Buhari Saƙo. Hoto: Muhammadu Buhari.
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Yan Ta’adda Sun Dasa Bam Ta Karkashin Kasa a Kaduna, Mutum 2 Sun Halaka

Wadannan matasan karkashin kungiyar Niger Delta Progressive Youth Forum sun ce gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ya nuna yana darajar rayuwakar al'umma ta hanya sadaukarwar da ya yi don tallafawa wadanda ambaliyar ya shafa.

Da ya ke magana yayin taron manema labarai a ranar Laraba, 2 ga watan Nuwamba, Richard Egbe wanda ya jagoranci matasan ya ce kimanin mutane 5,200 a yankin Neja Delta sun samu kayan tallafi daga NEMA.

Egba ya ce shugaban NEMA, Ahmed Habib, ya tafi yankin domin sanya ido kan yadda za a raba kayan tallafin ga mutanen da abin ya shafa, rahoton The Sun.

Kalamansa:

"Ya tabbatar an raba kayan tallafin a yankuna daban-daban da abin ya shafa, kamar yadda gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta umurta.
"Kayan tallafin da NEMA ta bada sun hada da ton 115 na masara, kimanin buhuna 6,100 na hatsin 70kg, Ton 99.7 na dawa wanda ya yi daidai da buhuna 2,774 na buhu mai nauyin 60kg da Ton 85.7 na Garri wanda ya kai 2,948 na 20kg."

Kara karanta wannan

Kwankwaso Bai Dauko Hayar Kowa Ba, Da Kansa Ya Tsara Manufofinsa Ga Yan Najeriya, NNPP

Ambaliyar Ruwa: Mutum 92 Sun Rasa Rayukansu Yayin da Gwamna Ya Lula Yawon Shakawata Ketare

A wani rahoton, kun ji cewa yawan wadanda ambaliyar ruwa yayi ajali a jihar Jigawa ya haura inda ya kai har mutum 92.

Wannan yana zuwa ne yayin da Gwamnan jihar Jigawa, Muhammad Badaru, yake shan caccaka sakamakon shillawa kasar waje da yayi hutu ba tare da ziyartar wadanda ibtila'in ya fadawa ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel