Kotu Ta Ayyana Ɗan Tsohon Gwamna A Matsayin Wanda Ya Ci Zaɓen Fidda Gwani Na APC A Babban Jihar Arewa

Kotu Ta Ayyana Ɗan Tsohon Gwamna A Matsayin Wanda Ya Ci Zaɓen Fidda Gwani Na APC A Babban Jihar Arewa

  • An ayyana Oluwasegun Adebayo, dan tsohon gwamnan jihar Kwara, Cornelius Adebayo, a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwani na Isin/Oke-Ero/Ekiti/Irepodun a jihar Kwara
  • Kotun ta soke zaben fidda gwani da ta bawa Raheem Olawuyi, dan majalisa da ke neman yin tazarce a jam'iyyar APC nasara
  • Adebayo ya fada wa kotu cewa Olawuyi ya yi takara na tikitin kujerar Kwara South a APC, inda ya sha kaye hannun Sanata Lola Ashiru yayin zaben fidda gwanin

Ilorin Kwara - Kotu ta soke zaben fidda gwani na mazabar Isin/Oke-Ero/Ekiti/Irepodun a jihar Kwara.

Babban kotun tarayya da ke zamanta a Ilorin, babban birnin jihar Kwara, ta soke zaben fidda gwanin ya ba bawa Raheem Olawuyi nasara a matsayin dan takarar APC na mazabar a zaben 2023, The Nation ta rahoto.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Gwamnonin APC 5 Na Tattaunawa da Atiku Abubakar

Buhari, Tinubu, Adamu
Kotu Ta Ayyana Ɗan Tsohon Gwamna A Matsayin Wanda Ya Ci Zaɓen Fidda Gwani Na APC A Babban Jihar Arewa. Hoto: Bola Ahmed Tinubu.
Asali: Facebook

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Olawuyi, dan majalisar wakilai na tarayya ne da ke neman yin tazarce a majalisar ta tarayya.

Zaben 2023 A Jihar Kwara

Kotun, amma ta ayyana abokin fafatawarsa kuma dan tsohon gwamna Cornelius Adebayo Oluwasegun a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwanin.

Adebayo ya garzaya kotu don kallubalantar nasarar Olawuyi, yana mai cewa an yi wasu kurakurai a zaben.

Ya shaidawa kotu cewa shine ainihin wanda ya lashe zaben fidda gwanin na APC a Isin/Oke-Ero/Ekiti/Irepodun.

Yan Majalisar Kwara A Zaben 2023

Dan tsohon gwamnan ya ce Olawuyi ya yi takarar tikitin sanata na Kwara South amma ya sha kaye a hannun Sanata Lola Ashiru a zaben cikin gida.

Bayan sauraron korafin, Mai sharia Mohammed Sani ya ayyana Adebayo a matsayin wanda ya yi nasara.

Alkalin ya jadada cewa dan tsohon gwamnan shine dan takarar APC na Isin/Oke-Ero/Ekiti/Irepodun a zaben majalisar tarayya na 2023.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Jam'iyyar APC Ta Saki Jadawalin Yakin Neman Zabenta Na Shugaban Kasa

Zaben 2023: Mataimakiyar Kakakin APC Ya Bayyana Jihohin Arewa Da Obi Zai Iya Cin Zabe

Duba da kara karbuwa da Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party, LP, ke kara samu, jam'iyyar APC ta yi wani hasashe kan wasu abubuwa da ka iya faruwa a babban zaben 2023.

Mataimakiyar kakakin kungiyar kamfen din shugaban kasa na APC, Hannatu Musawa, wacce ta yi magana da The Punch a ranar Lahadi, 16 ga watan Oktoba ta ce akwai yiwuwar Obi ya samu kuri'un wasu jihohin arewa da kowane dan takara ke bukata don cin zabe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel