Bayan Ya Gama Ragargazar Shugaban PDP, Gwamna Wike Ya Dura Kan Jagoran Jam’iyya

Bayan Ya Gama Ragargazar Shugaban PDP, Gwamna Wike Ya Dura Kan Jagoran Jam’iyya

  • Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya cigaba da ragargazar duk wanda ya ja da shi a jam’iyyar PDP
  • Nyesom Wike ya soki Dele Momodu saboda ‘dan siyasar ya nemi ya goyi bayan Atiku Abubakar a 2023
  • Mai girma Gwamnan yace Momodu sabon shiga PDP ne, ya kira shi mai neman suna kuma maras aikin yi

Rivers - Nyesom Wike na jihar Ribas ya yi wa Dele Momodu wulakanci a game da rikicin cikin gidan da ake fama da shi a jam’iyyar adawa ta PDP.

The Cable tace Gwamna Nyesom Wike ya caccaki Dele Momodu bayan wasu kalamai da ya yi, inda ya nemi ‘yan PDP su goyi bayan Alhaji Atiku Abubakar.

Da ya zanta da ‘yan jarida, Momodu ya yabi ayyukan da Gwamnatin Wike take yi, ya kuma ce ya rubutawa Gwamnan takarda, yana rokon su taimaki PDP.

Kara karanta wannan

PDP Za ta Ci Duka Zaben da Za Ayi, Ban da na Kujerar Shugaban kasa Inji Gwamnanta

Amma da ya tashi maida martani, Nyesom Wike ya yi amfani da kakkausan harshe, ya nuna Dele Momodu ba kowa ba ne a tafiyar jam’iyyar hamayyar.

Wike ya yi wa ‘dan jaridar gorin zama ‘dan jam’iyya, ya kuma nuna bai da nauyi a siyasa domin ko a jiharsa bai iya samun kuri’a a zaben tsaida gwani ba.

Nyesom Wike
Gwamna Nyesom Wike Hoto: @GovWike
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Raddin da Nyesom Wike ya yi

“Na karanta na ji wasu mutane su na cewa ka da mu wuce gona da iri. A gaskiya bai kamata in maida martani a kan irin wannan batu ba.
Na karanta, na ji an ce wani Dele Momodu ne. irin wadannan ne abubuwan da nake magana a kai. Tambaye shi, yaushe ya shigo jam’iyyar?
Ya zo PDP ne makonni biyu kafin a shiga zaben ‘dan takarar shugaban kasa. Daga jihar Edo yake, ko kuri’a daya bai samu ba, ko daya!

Kara karanta wannan

Ganduje Ba Zai Ruguza Mani Gida ba, ko da a kan Layin Lantarki aka Gina Inji Rarara

Idan ba ka da aikin yi, kayi magana - Wike

Kawai kana neman a san ka – Daga mai neman shugaban kasa zuwa kakaki – Mai neman mulkin Najeriya ya zama mai magana da yawu.

Kamar yadda za a ji a wani bidiyo a Twitter, Wike yace Momodu bai da aikin yi ne, yace shi yana da abin yi, ba zai bari ayi amfani da shi wajen shahara ba.

Legit.ng ta rahoto Wike yana mai cewa Dele Momodu ya zo garin Fatakwal bila-adadin domin kaddamar da irin ayyukan da gwamnatinsa ta yi a jihar.

PDP za tayi nasara amma ban daa ....

A yau aka samu rahoto Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike yayi hasashen galaba a duka kujerun majalisar dokoki, majalisun wakilai, Sanatoci, da Gwamna.

Amma kuma Mai girma Gwamnan yace sai an yi gyara kafin jam’iyyar PDP ta ci zaben Shugaban kasa a jihar Ribas, alamar bai tare da Atiku Abubakar har yau.

Kara karanta wannan

Ka yi kadan: Gwamna Wike Ya Aikawa Shugaban Jam’iyyar PDP Sabon Raddi

Asali: Legit.ng

Online view pixel