Ganduje Ba Zai Ruguza Mani Gida ba, ko da a kan Layin Lantarki aka Gina Inji Rarara
- Dauda Adamu Kahutu yace har yanzu akwai kyakkyawar alaka tsakaninsa da Abdullahi Umar Ganduje
- Ana zargin mawakin da cin mutuncin Gwamnonin jihar Kano idan ya fahimci mulkinsu ya zo gaban goshi
- Rarara yace bai fi karfin doka ba, amma yace gidan da yake zama yana da cikakken iznin Gwamnati
Kano - Dauda Adamu Kahutu wanda aka fi sani da Rarara, ya yi hira da gidan yada labarai na DCL Hausa, ya yi karin haske kan rikicin da ake yi da shi.
Legit.ng Hausa ta saurari gabar wannan tattaunawa, inda ta ji mawakin yana watsi da rade-radin da ake yi na gwamnatin jihar Kano za ta rusa masa gida.
Dauda Adamu Kahutu ya amsa tambaya game da zargin da ake yi masa na fita daga jam’iyyar APC ko kuma akalla zai yi wa tsarin wake da shinkafa a 2023.
“Idan ba na nan, za a san ba na nan. Mutum dubu za su je taro, wani ma ba a san ya je ba. Amma idan Rarara ya je, za a ce ya je, idan bai je ba, za a ce bai je ba.
Duk Bahaushe ya san abin da nake nufi. Ni ina jam’iyyar APC, da na bar APC da ka ji labari.”
- Dauda Adamu Kahutu
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Na rabu da maganar yin SAK
“Ni, ni babu wata takaddama ko wani abin. Magana ce kawai ta na ce ina yin Sha’aban Sharada."
- Dauda Adamu Kahutu
Mawakin yace a dalilin goyon bayan takarar Sha’aban Sharada a jam’iyyar adawa ta ADP, wasu suke ta zuga, suna so a tursasa shi ya yi jam’iyyar APC sak.
Rarara ya shaidawa DCL Hausa yana cikin wadanda suka amsa kiran Mai girma Muhammadu Buhari na yin sak, amma a karshe hakan ya kawo sakarkaru.
A dalilin illar zaben APC daga sama har kasa, shahararren mawakin yace a zabe mai zuwa ya kamata jama’a su zabi cancanta, su daina bin jam’iyya a makance.
Za a rusawa Rarara gida?
Da yake bayani kan batun ruguza masa gida, Attajirin mawakin yace gwamnatin Kano ba za ta rusa masa gida ba, ko da kuwa a kan layin lantarki aka yi ginin.
A hirar, an ji mawakin yana cewa baya ga Murtala Garo, ya fi kowa shan wahala a tafiyar Ganduje, don haka ko an rusa masa gida, gwamna zai sake gina masa.
Rarara yace bai fi karfin doka tayi aiki a kansa ba, amma gwamnati ta bi doka wajen gina gidan.
Ina tare da Ganduje - Rarara
Dauda Kahutu ya musanya zargin da ake yi masa na cin zarafin Gwamnoni da zarar wa’adinsu ya zo karshe, yace mutane ba su fahimtar Hausar da yake yi a waka.
A cewar Rarara, har yau yana tare da Abdullahi Ganduje sai dai idan gwamnan ya ja layi, yace amma akwai masu munafunci domin a hada shi fada da gwamnati.
APC za ta doke PDP a 2023
Dazu an ji labari Dayo Israel yana sa ran Bola Ahmed Tinubu zai doke Wazirin Adamawa, Atiku Abubakar a jiharsa ta Adamawa a zaben shugaban kasa.
Bayan ya karbi dinbin mutanen da suka bar jam’iyyar PDP, Shugaban matasan jam’iyyar APC na Najeriya yace APC ce za tayi nasara daga kasa har sama.
Asali: Legit.ng