CUPP: Shugaban PDP ya Kitsa Yadda Masu Rigima da Shi a Jam’iyya Za Su Kashi a Zabe

CUPP: Shugaban PDP ya Kitsa Yadda Masu Rigima da Shi a Jam’iyya Za Su Kashi a Zabe

  • Kungiyar CUPP tayi wa Shugaban PDP na kasa watau Iyorchia Ayu raddi, bayan wasu kalaman shi
  • Maganar da Dr. Iyorchia Ayu ya yi na hana mutum tsayawa takara a zabe ya jawo masa sukar CUPP
  • Kakakin kungiyar, Ikenga Imo Ugochinyere yana ganin shugaban jam’iyyar yana neman kashe PDP

Abuja - Kungiyar hadakar jam’iyyun siyasa a Najeriya ta CUPP, ta fito tana zargin shugaban PDP, Iyorchia Ayu da cewa zai hargitsa jam’iyyar.

Vanguard ta rahoto Mai magana da yawun kungiyar CUPP, Ikenga Imo Ugochinyere yace dole ne ayi waje da Iyorchia Ayu daga jam’iyyar PDP.

A cewar Ikenga Imo Ugochinyere, Dr. Ayu ya kama hanyar ruguza babbar jam’iyyar hamayyar ne, yana yakar duk wadanda suke rikici da shi.

A wani jawani da ya fitar a Abuja, kakakin na CUPP yace cigaba da zama da Ayu yake yi a matsayin shugaban jam’iyya, zai raza masu kada kuri'a.

Kara karanta wannan

APC da Tinubu Na Shirin Ba Atiku Mamaki a Adamawa, Za a Tika Shi da Kasa a Mahaifa

An maidawa Ayu martani

Wannan jawabi raddi ne ga shugaban jam’iyyar na kasa bayan yace yana da ikon da zai hana mutum shiga takaran da za ayi a karkashin PDP.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Ba na shakkar cewa Ayu ya na nufin ruguza jam’iyyar PDP ne. Shiyasa ya dage ya cigaba da zama a kujerarsa duk da ana kiran ya sauka.
Shugaban PDP
Shugabannin PDP na kasa Hoto: @IyorchiaAyu
Asali: Twitter

Masifar son shugabancinsa yana razana matasan da suke yin zabe.
Na gamsu cewa Ayu yana shirya yadda zai ga bayan ‘yan takaran PDP da ke adawa da shi. Wannan karara yake a jawabin da ya yi a ranar Juma’a a Benuwai.
Kataborar da ya yi a Benuwai shi ne babban dalilin da ya sa ya kamata ya sauka daga mukaminsa. - Ikenga Imo Ugochinyere

Ba ka da wannan ikon a doka

Da yake bayani, Sun ta rahoto Ugochinyere yace Ayu bai da ikon da zai takawa ‘dan takara burki, yace ko da ya yi hakan, kotu za ta tabbatar da gaskiya.

Kara karanta wannan

Ka yi kadan: Gwamna Wike Ya Aikawa Shugaban Jam’iyyar PDP Sabon Raddi

Ugochinyere ya ba tsohon Sanatan shawarar ya yi murabus, kuma kafin a kai ga lokacin nan, ya guji irin wadannan kalamai marasa dadi da yake yi.

Martanin da Wike ya yi

An ji labari Gwamna Nyesom Wike ya maida martani ga jawabin da aka ji shugaban jam’iyyar PDP na kasa ya yi a kan hana wasu shiga takara a zaben badi.

Iyorchia Ayu ya yi ikirarin zai iya hana mutum takara, amma Wike yace Ayu bai da wannan iko, ya kalubalance shi da ya karbe tikitin 'Yan takaran Ribas.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng