Hotonan Ganawar Dan Takarar Shugaban Kasa Peter Obi da Sheikh Dahiru Bauchi

Hotonan Ganawar Dan Takarar Shugaban Kasa Peter Obi da Sheikh Dahiru Bauchi

  • Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour na yin duk mai yiwuwa don ganin ya gaji kujerar Buhari a 2023
  • Tsohon gwamnan na Anambra ya kai wata ziyara ga sarkin Bauchi da kuma fitaccen malamin addinin Islama na Afrika Sheikh Dahiru Usman Bauchi
  • An ga hotunan lokacin da Obi ya ziyarci Sheikh a Bauchi tare da abokin gaminsa, Dr Yusuf Datti Baba-Ahmed

Jihar Bauchi - Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour na kara tsawon kafa da hannu wajen tallata kansa a fadin kasar nan gabanin zaben 2023.

Obi da abokin gaminsa, Dr Yusuf Datti Baba-Ahmed sun kai wata ziyara a jihar Bauchi, inda suka gana da babban malamin addini na Afrika, Sheikh Dahiru Usman Bauchi.

Kara karanta wannan

An tura N4.6bn wani asusu a mulkin Jonathan, EFCC ta fadi dalilin da yasa bata tuhume shi ba

Peter Obi ya gana da Sheikh Dahiru Bauchi
Hotonan Ganawar Dan Takarar Shugaban Kasa Peter Obi da Sheikh Dahiru Bauchi | Hoto: @PeterObi
Asali: Twitter

Tsohon gwamnan na Anambra ya yada hotunan wannan ziyarar da ya kai ga malamin a shafinsa na Twitter a yau Juma'a 28 ga watan Oktoba.

Ya rubuta cewa:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Yayin da muka je Bauchi, Dr Yusuf Datti Baba-Ahmed da ni mun gana da Sheikh Dahiru Usman Bauchi."

Obi ya gana da sarkin Bauchi

Hakazalika, a wata ziyarar, Peter Obi ya bayyana cewa, ya kai ziyara fadar sarkin Bauchi domin neman tabarruki a tafiyarsa ta neman gaje Buhari a 2023.

Ya rubuta a shafinsa na Twitter cewa:

"A baya-bayan nan, ni da Dr Yusuf Datti Baba-Ahmed mun gana da sarkin Bauchi, HRH Dr. Rilwanu Suleiman Adamu a lokacin da muka kai ziyara jihar Bauchi."

'Yan siyasa da dama a Najeriya na ci gaba da yawon kamfen da kai ziyarar neman iri gabanin saukar daminan zaben 2023.

Kara karanta wannan

NNPP ta fadi dalilan da suka sa Kwankwaso ya ki martaba gayyatar dattawan Arewa

Tinubu da Na Son Kai, Ba Zan Zabe Shi Ba a Zaben 2023, in Ji Farfesa Akintoye

A wani labarin, gabanin zaben 2023 na shugaban kasa, farfesa Banji Akintoye, shugaban kungiyar Yarbawa ta Yoruba Nation Self-Determination Struggle ya bayyana kadan daga halin dan takarar shugaban kasa na APC.

Ya kuma bayyana cewa, tabbas ba zai zabi Bola Ahmad Tinubu ba saboda wasu dalilai da ya bayyana.

A cikin wata sanarwar da jaridar Punch ta wallafa a ranar Alhamis 27 ga watan Oktoba, farfesa Akintoye ya ce Tinubu na son zama shugaban kasa ne kawai don cimma wata manufa ta kashin kai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel