Dalilin da Ya Sa Ba Mu Gayyaci Jonathan Don Yi Masa Tambayoyi Ba, Inji Shaida Daga EFCC

Dalilin da Ya Sa Ba Mu Gayyaci Jonathan Don Yi Masa Tambayoyi Ba, Inji Shaida Daga EFCC

  • An zauna kotu kan batun da ya shafi shari'ar almundahana tsakanin EFCC da wasu jiga-jigan gwamnatin Jonathan
  • An bayyana wasu kudaden da suka kai N4.6bn da ake kyautata zaton an yi amfani dasu ne wajen kamfen a 2015
  • Hakazalika, shaidan da aka gabatar ya bayyana dalilin da yasa ba a gayyaci tsohon shugaban kasa don yin bahasi ba

FCT, Abuja - Jami'in titsiye na hukumar EFCC, Shehu Shuaibu ya bayyana cewa, wasu kudade N4.6bn da ake zargin an tura asusun hadin gwiwa an yi amfani dasu ne wajen yin kamfen din takarar shugaban kasa na Goodluck Jonathan a 2015, rahoton Punch.

Shu'aibu ya bayyana hakan ne a gaban mai shari'a Daniel Osiagor a shaidar da ya gabatar kan shari'ar tsohon ministan kudi, Sanata Nenadi Usman, tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode da wasu mutum bisa zargin almundahana.

Kara karanta wannan

Nnamdi Kanu Ya Shigar da Karar Gwamnatin Buhari, Yana Neman a Biya Shi N100bn

EFCC ta fadi dalilin da yasa bata kama Jonathan ba
Dalilin da Ya Sa Ba Mu Gayyaci Jonathan Don Yi Masa Tambayoyi Ba, Inji Shaida Daga EFCC | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Da yake jawabi, lauyan Usman, Mr Ferdinand Orbih (SAN) ya ce a iyakar binciken da hukumar EFCC ta yi, bata taba gayyatar tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ba.

Shaidan ya kuma bayyana cewa, Nenadi Usman ya kasance daraktan kudi na kungiyar kamfen din Jonathan a wancan lokacin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hakazalika, ya shaida cewa, Femi Fani-Kayode ya kasance daraktan yada labarai na tafiyar gangamin Jonathan a 2015.

Me yasa ba a gayyaci Jonathan ba?

Da aka tambaya me yasa ba a gayyaci Jonathan don ba da shaidar shigar kudi asusun ba, sai ya ce:

"A'a, bamu gayyace shi, tunda shugaban kasan ba shine ya kashe kudin ba."

Yayin da mai shari'a ya tambaya ko an kamo wadanda suka tura kudin zuwa asusun kuma an gurfanar dasu, sai shaidan kotu yace bai san ya zuwa yanzu me aka yi a kansu ba, rahoton The Nation.

Kara karanta wannan

NNPP ta fadi dalilan da suka sa Kwankwaso ya ki martaba gayyatar dattawan Arewa

Bayan jin batutuwa da dama da suka shafi shaida kan shair'ar, mai shari'a ya dage ci gaba da sauraran karar sai ranar Juma'a 28 ga watan Oktoba.

Tinubu da Na Son Kai, Ba Zan Zabe Shi Ba a Zaben 2023, in Ji Farfesa Akintoye

A wani labarin, gabanin zaben 2023 na shugaban kasa, farfesa Banji Akintoye, shugaban kungiyar Yarbawa ta Yoruba Nation Self-Determination Struggle ya bayyana kadan daga halin dan takarar shugaban kasa na APC.

Ya kuma bayyana cewa, tabbas ba zai zabi Bola Ahmad Tinubu ba saboda wasu dalilai da ya bayyana.

A cikin wata sanarwar da jaridar Punch ta wallafa a ranar Alhamis 27 ga watan Oktoba, farfesa Akintoye ya ce Tinubu na son zama shugaban kasa ne kawai don cimma wata manufa ta kashin kai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel