Kwankwaso Na da Kwararan Dalilai Na Kin Amsa Gayyatar Dattawan Arewa, Jigon NNPP

Kwankwaso Na da Kwararan Dalilai Na Kin Amsa Gayyatar Dattawan Arewa, Jigon NNPP

  • Mai magana da yawun jam'iyyar NNPP ya magantu kan dalilin da yasa Kwankwaso ya ki amsa gayyatar dattawan Arewa
  • An gayyaci Kwankwaso da sauran 'yan takarar shugaban kasa domin tattauna makomar zaben 2023 mai zuwa
  • Ana ci gaba da shirye-shiryen babban zaben 2023, lamarin dake kara jawo hankulan 'yan Najeriya wuri guda

FCT, Abuja - Ladipo Johnson, mai magana da yawun jam'iyyar NNPP ya bayyana cewa, dan takarar shugaban kasan jam'iyyar na da dalilansa na kin amsa gayyatar dattawan Arewa, Daily Trust ta ruwaito.

Gamayyar kwamitin dattawan Arewa sun gayyaci dan 'yan takarar shugaban kasa daga jam'iyyu daban-daban domin wata tattaunawa ta musamman dasu kan zaben 2023 mai zuwa.

Kwankwaso na da dalilin kin amsa gayyatar dattawan Arewa, inji mai magana da yawun NNPP
Kwankwaso Na da Kwararan Dalilai Na Kin Amsa Gayyatar Dattawan Arewa, Jigon NNPP | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

'Yan takarar da aka gayyata sun hada da Bola Tinubu na APC, Atiku Abubakar na PDP, Rabiu Kwankwaso na NNPP, Peter Obi na LP, Kola Abiola na PRP da Adewole Adebayo na DP.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Kwankwaso Ya Bayyana Ranar Da Zai Gabatar Da Manufofinsa Ga Yan Najeriya

Kwankwaso ya yi abin da ya dace, inji jigon NNPP

Ya yake kare mai gidansa Kwankwaso yayin wata tattaunawa da gidan talabijin na Channels, Johnson ya ce hakan da ya yi shine abin da ya dace.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A kalamansa:

"Lokacin da lamarin ya faru kamar yadda na fada a wani lokaci, akwai sanarwa mai shafi hudu a kasa. Ku tuna cewa, ya ki amsa gayyatar tun kafin wannan taron.
"Hakan ya faru ne saboda yana kwakkwaran dalilin cewa, wasu dake da hannu a ganawar suna goyon bayan daya daga cikin 'yan takarar."

Hakazalika, ya tuna yadda Kwankwaso ya sha fama a hannun wasu daga cikin wadanda suka shirya wannan tattaunawa a 2019.

Ya kara da cewa, da Kwankwaso ya halarci zaman, da an samu faruwar wani abin da ba lallai ya zama mai dadi ba.

Kara karanta wannan

Rudani: Gwamnan PDP mai ba Atiku ciwon kai ya zabo tsohon jigon APC ya zama kwamishinansa

John ya kara da cewa, Kwankwaso ba zai taba janyewa wani ba a burinsa na zama shugaban kasa a zaben 2023 mai zuwa.

Tsohon Kakakin Jam’iyyar PDP, Olisa Metuh, Ya Yi Murabus Daga Jam’iyyar

A wani labarin, Cif Olisa Metuh, tsohon sakataren yada labaran jam'iyyar PDP ya bayyana yin murabus daga jam'iyyar baki daya domin ya dukufa a wasu lamurran na daban.

A cikin wata wasika da ya turawa shugaban jam'iyyar na kasa, Iyochia Ayu mai kwanan watan Talata 25 ga watan Oktoba, Metuh ya ce a nan gaba zai mayar da hankali ne da ba da gudunmawa ba tare da kasancewa dan siyasa ba, rahoton Leadership.

A wasikar, tsohon jigon na PDP ya bayyana imaninsa cewa, zai ba da gudunmawarsa sosai a fannin dimokradiyya da gwamnati mai inganci a Najeriya yayin da ya koma gefen siyasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel