Tsohon Kakakin Jam’iyyar PDP, Olisa Metuh, Ya Yi Murabus Daga Jam’iyyar

Tsohon Kakakin Jam’iyyar PDP, Olisa Metuh, Ya Yi Murabus Daga Jam’iyyar

  • Tsohon kakakin jam'iyyar PDP na kasa, Olisa Metuh ya lallaba ya fice daga jam'iyyar tare da yin sallama da siyasa
  • Metuh ya bayyana ra'ayin cewa, zai ba Najeriya da shugabanci gudunmawarsa amma ba ya bukatar ci gaba da zama dan siyasa
  • Tsohon jigon siyasan ya kuma shaida cewa, ya ji dadin kasancewa a jam'iyyar PDP kuma zai dade yana tuna alheranta

Abuja - Cif Olisa Metuh, tsohon sakataren yada labaran jam'iyyar PDP ya bayyana yin murabus daga jam'iyyar baki daya domin ya dukufa a wasu lamurran na daban.

A cikin wata wasika da ya turawa shugaban jam'iyyar na kasa, Iyochia Ayu mai kwanan watan Talata 25 ga watan Oktoba, Metuh ya ce a nan gaba zai mayar da hankali ne da ba da gudunmawa ba tare da kasancewa dan siyasa ba, rahoton Leadership.

Kara karanta wannan

"Dalilin Da Yasa Cikin Sauki Tinubu Zai Lallasa Atiku, Ya Lashe Zaben Shugaban Kasan 2023"

Olisa Metuh ya hakura da siyasa, ya fita a jam'iyyar PDP
Tsohon Kakakin Jam’iyyar PDP, Metuh, ya yi murabus daga Jam’iyyar | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Dalilin da yasa Metuh ya ajiye batun siyasa

A wasikar, tsohon jigon na PDP ya bayyana imaninsa cewa, zai ba da gudunmawarsa sosai a fannin dimokradiyya da gwamnati mai inganci a Najeriya yayin da ya koma gefen siyasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Metuh ya kuma bayyana kansa a matsayin mafi jimawan mamban NEC na PDP da aka zaba, kuma zai ci gaba da tuna alheran da ya samu a jam'iyyar PDP na tsawon rayuwarsa.

A wasikar da jaridar Daily Sun tace ta samo, Metuh ya ce:

"A tafiyar da na yi ta makwanni uku na rashin lafiya, na zo na gane ba zai yiwu a ci gaba da damuwa dani a siyasar Najeriya ba.
"Dalilin wannan shawari kuwa ya zo ne daga kwarewa da kuma dabi'ar siyasa da ci gaban Najeriya, na yi imanin zan ba da gudunmawa a dimokradiyya da gwamnati mai inganci a Najeriya ba tare da zama dan siyasa ba."

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Peter Obi Ya Ce Ko Ƴaƴan Cikinsa Ba Su Yarda Da Shi Idan Ya Yi Alƙawari, Mutane Sun Yi Martani

Alaka Ta Da Buhari Itace Ta Gaskiya, Kuma Abin Koyi, Inji Osinbajo

A wani labarin, mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo ya yaba da irin alakar dake tsakaninsa da uban gidansa shugaba Muhammadu Buhari, tare da kwatanta alakar da cewa sahihiyace kuma abin koyi.

Osinbajo ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin kaddamar wani littafin gwamna Ganduje na jihar Kano, kamar yadda Channels Tv ta ruwaito.

Ya kuma bayyana dalilin da yasa shugabannin siyasa da mataimakansu ke gina sahihiyar alaka a tsakanin juna. Mataimakin shugaban kasan ya kuma bayyana cewa, shi dai ya fi sauran mataimakan sa'ar samun uban gida.

Asali: Legit.ng

Online view pixel