Zan Yi Kamfen da Lambar Yabon da Shugaba Buhari Ya Bani, Inji Gwamnan PDP Wike

Zan Yi Kamfen da Lambar Yabon da Shugaba Buhari Ya Bani, Inji Gwamnan PDP Wike

  • Gwamnan jihar Ribas ya bayyana irin shirin da yake dashi a zaben 2023 mai zuwa bayan karbar lambar yabo daga Buhari
  • Gwamnan ya ce zai yi amfani da wannan lambar yabo domin yin kamfen a zaben 2023 mai zuwa nan kusa
  • Wike ya kuma nuna cewa, Allah ne ke ba da mulki, don haka bai yiwa wani alkawarin zama gwamna ba

Jihar Ribas - Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ya bayyana cewa, zai yi amfani da lambar yabon da shugaban kasa Muhammadu ya bashi wajen yakin neman zaben 2023, Punch ta ruwaito.

Wike ya bayyana hakan ne a wani taron nuna lambar yabon da Buhari ya bashi, wanda aka gudanar a babban birnin jiharsa, Fatakwal a daren jiya Litinin 24 ga watan Oktoba.

Yayin da yake sadaukar da lambar yabon ga ubangiji, ya kuma shaida cewa, gwamnatinsa ta samu nasarar yin ayyukan more rayuwa ne saboda kwarin gwiwar da yake samu daga mutanen jihar.

Kara karanta wannan

Rudani: Gwamnan PDP mai ba Atiku ciwon kai ya zabo tsohon jigon APC ya zama kwamishinansa

Gwamna Wike ya fadi abin da zai yi da lambar yabon da Buhari ya bashi
Zan Yi Kamfen da Lambar Yabon da Shugaba Buhari Ya Bani, Inji Gwamnan PDP Wike | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

A kalamansa:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Dole ne mu yi aiki tare. Sarakunan gargajiya, ku taimaki Ribas ta samu ci gaba. 'Yan kwangila, dukkanku ya kamata ku taimakawa jihar Ribas domin jihar Ribas ta zama abin da take son zama, tubalin da Dr Peter Odili ya kafa."

Babu wanda na yiwa alkawarin zama gwamnan Ribas

A bangare guda, gwamna Wike ya ce bai taba yiwa wani alkawarin kujerar gwamna ba, tare da yin ishara da cewa, Allah ne ke ba da mulki ga wanda yaso.

Ya kuma ci fariyar cewa, zai sauka daga mukaminsa na gwamna idan wani yazo yace ya yi masa alkawari sannan ya gaza cikawa.

A cewar Wike:

"Na sha fadawa mutane na Allah ne ke ba da mulki. Babu wata rana da na taba zama da wani. Ina kalubalantar duk wanda yace na zauna dashi, kuma na yi mishi alkawarin zai zama gwamna.

Kara karanta wannan

2023: Gwamnan PDP ya tona asirin APC, ya fadi mummunan abin da zai faru idan Tinubu ya ci zabe

"Idan wani zai fito ya kuma kalubalance ni, zan yi murabus daga mukamin gwamnan jihar Ribas."

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba wasu jiga-jigan gwamnatin da suka ba da gudunmawa ga ci gaban kasa lambobin yabo a makon jiya, rahoton This Day.

Tsohon Jigon APC a Ribas Chris Finebone Ya Fito a Jerin Sabbin Kwamishinonin Wike

A wani labarin, Mr. Chris Finebone, tsohon kakakin APC a jihar Ribas ya fito a jerin sunaye 18 na sabbin kwamishinonin da gwamnan PDP Wike ya mika majalisar dokokin jiharsa domin tantancewa.

Finebone, wanda dan a mutun minista kuma tsohon gwamna Rotimi Amaechi na APC ne ya kasance mai tsananin suka ga tafiyar gwamnatin Nyesom Wike na PDP.

Sai dai, an samu rahotannin dake bayyana cewa, Finebone ya sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP a baya, kamar yadda PM News Nigeria ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.