Dan Takarar APC Tinubu Ya Gana da Malaman Addinin Kirista a Jihar Kano, Ya Yi Musu Jawabi
- Wani bidiyon da aka yada ya nuna lokacin da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Bola Ahmad Tinubu ke yiwa wasu malaman addinin kirista jawabi
- A jawabin Tinubu, ya bayyana kadan daga abin da ya sa a rai kan yadda addinai suke a Najeriya, kuma da fahimtarsa
- Tinubu na ci gaba da fuskantar damuwa daga kiristocin Arewa tun bayan da ya zabo Kashim Shettima a matsayin abokin takara
Jihar Kano - Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmad Tinubu ya gana da wasu manyan malaman addinin kirista a jihar Kano ta Arewa maso Yammacin Najeriya.
A wani bidiyon da aka yada na Tinubu, an bayyana lokacin da yake yi musu jawabi game da hadin kai da kuma zaman lafiya da kamanceceniya tsakanin Musulmi da Kirista a Najeriya.
Tinubu ya bayyana cewa, hanya daya Musulmai da Kiristoci ke bi wajen neman gafara, kamar dai yadda yazo a Al-Qur'ani a cewarsa.
Ya kuma yi tsokaci cewa, a gabansa aka ba matarsa sandar zama fasto, don haka yana kaunar kowa, kuma zai yi tafiya da dukkan addinai.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A bidiyon da aka yada a Twitter an ji Tinubu ya yi bayani, inda yake cewa:
"Yadda kuke neman gafara, haka muma muke neman gafara a cikin Al-Qur'ani mai girma. Ranar da aka ba matata mukamin fasto, ina wurin."
Matsalar Tinubu da kiristocin Arewa
Tinubu dai na ci gaba da shan kira daga kiristocin Arewacin Najeriya da ya gaggauta sauya abokin takararsa tare da dauko wanda ba Musulmi don kiyaye martabar kowane addini.
Idan baku manta ba, Bola Ahmad Tinubu, wanda tsohon gwamnan Legas ne ya zabo Kashim Shettima a matsayin abokin takara, wanda kuma Musulmi ne tare da kasancewa Bola Musulmi.
An saba samun dan takara Musulmi da abokin takara kirista ko dan takara kirista abokin takara Musulmi, amma akan yi cece-kuce a Najeriya duk sadda aka samu 'yan addini daya sun yi takara tare.
Najeriya Za Ta Wargaje Idan Tinubu da APC Suka Ci Zabe a 2023, Inji Gwamnan PDP Obaseki
A wani labarin, gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki ya gargadi 'yan Najeriya a ranar Litinin cewa, idan suka sake APC ta sake komawa mulki, to tabbas kasar za ta wargaje.
Obaseki ya bayyana hakan ne a bikin kaddamar majalisar kamfen din jam'iyyarsu ta PDP a jihar, kamar yadda Channels Tv tace ta samo.
Gwamnan ya kuma bayyana cewa, babu wanda notunan kansa ke daure da zai amince ya zabi Tinubu da APC a zaben da za a yi nan da watanni hudu a kasar nan.
Asali: Legit.ng