2023: Nan Ba Da Jimawa ba Yan Obidient Zasu Gaji, Ba Inda LP Zata Je, Obaseki
- Gwamnan Edo dake kudu maso kudancin Najeriya, Godwin Obaseki, ya kaddamar kwamitin kamfen PDP na jiharsa
- Da yake tsokaci, Obaseki yace mabiyan Peter Obi ba zasu kai labari ba, duk wannan tururin da suke mai gushewa ne
- Gwamnan yace ba ɗan Najeeiya mai cikakken tunani da zai kaɗa wa APC da Tinubu kuri'arsa
Edo - Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya kore duk wata damar samun nasara ga jam'iyyar Labour Party da ɗan takarar shugaban ƙasa, Peter Obi, a babban zaɓen 2023.
Channels TV ta rahoto cewa Obaseki ya bayyana haka ne a wurin kaddamar da kwamitin yakin neman zaɓen jam'iyyar PDP na jiharsa ranar Litinin.
Gwamnan yace mabiyan Peter Obi waɗanda suka yi ƙaurin suna da "Obidients" nan ba da jimawa ba zasu rasa wannan tururin da zumudin da suke yi.
Vanguard ta rahoto Obaseki yace:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Mutanen dake ikirarin su masu biyayya ne, hakan zata iya yuwuwa amma nan ba da jimawa ba duk wannan kunfar bakin da suke zata lafa. Mun san yadda zamu tafiyar da zaɓe, mutum nawa ne zasu iya abinda muka yi?"
"Saboda haka wannan zaɓen na mu ne kuma da ikon Allah ba zamu sha ƙasa ba. A yanzu muna son gaggauta kammala shirin mu daga nan kuma sai mu diba yadda zamu taimaki sauran jihohin PDP."
Najeriya zata wargaje idan Tinubu ya ci zaɓe - Obaseki
Ya kuma ƙara da cewa babu wani ɗan Najeriya mai cikakken hankali da tunani mai kyau da zai zaɓi jam'iyyar APC da ɗan takararta na shugaɓan ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
A cewar gwamna Obaseki na jihar Edo, jihar dake kudu maso kudancin Najeriya, yace ƙasar nan ka iya tarwatse wa idan APC ta lashe zaɓen shugaban kasa mai zuwa.
A wani labarin kuma Gwamna Wike Ya Fallasa Abinda Atiku Ya Masa a Ribas, Yace Ba Zai Masa Kamfen Ba a 2023
Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, yace ba zai yi wa ɗan takarar jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar yaƙin neman zaɓe ba.
Gwamna Wike wanda ya jima ba ya ga maciji da tsagin Atiku, yace ɗan takarar ya zaɓi makiyan Ribas a tawagar kamfe ɗinsa.
Asali: Legit.ng