Gwamnatin Najeriya Za ta Kashewa Jonathan, Obasanjo da su IBB N13.8bn a 2023

Gwamnatin Najeriya Za ta Kashewa Jonathan, Obasanjo da su IBB N13.8bn a 2023

  • Abin da aka warewa domin tsofaffin shugabannin Najeriya a kasafin kudin badi ya haura N13.80bn
  • Tsofaffin shugabannin farar hula da na sojoji da duka mataimakansu da ke raye za su karbi fansho
  • Tsofaffin sakatarorin din-din-din da shugabannin ma’aikatan gwamnatin tarayya za su tashi da N10bn

Abuja - N13,805,814,220 shi ne abin da aka ware a matsayin fanson tsofaffin shugabannin kasar nan da kuma mataimakansu a shekara mai zuwa.

Rahoton Punch yace a cikin wannan kudi ne za a biya tsofaffin shugabannin ma’aikatan gwamnatin tarayya da duk wasu sakatarorin din-din-din.

Wadanda za su amfana da wadannan kudi sun hada da duk wanda ya taba mulkar Najeriya irinsu Cif Olusegun Obasanjo da Dr. Goodluck Ebele Jonathan.

Tsofaffin shugabanni na zamanin soja kamar su Janar Yakubu Gowon, Janar Ibrahim Babangida da Janar Abdusalami Abubakar za su amfana da kudin.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Buhari Ya Sha Alwashin Yi wa Tinubu Gagarumin Kamfen

#2 za su samu fansho

Rahoton yace daga kason ne za a biya Commodore Ebitu Ukiwe (retd.) da duk wani takwaransa da ya zama na biyu a lokacin sojoji suna rike da kasar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Atiku Abubakar da Namadi Sambo wadanda sun rike kujerar mataimakan shugaban kasa daga 1999-2007 da 2010-2015 suna da kaso a kasafin shekarar badi.

Tsofaffin shugabannin kasa
Taron majalisar kolin Najeriya Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

Jaridar tace babu tabbacin Muhammadu Buhari da mataimakinsa, Yemi Osinbajo suna cikin wadanda za a biya kudin domin za su bar mulki a Mayu.

Tsofaffin ma'aikatan gwamnati za su gwangwaje

Tsofaffin shugabannin ma’aikatan gwamnati da wadanda suka taba rike sakataren din-din-din a Najeriya za su tashi da N10.5bn daga cikin kason kudin.

N1bn zai tafi wajen biyan kudin sallamar tsofaffin shugabannin hukumomin gwamnatin tarayya.

Hakan ba daidai ba ne - Masana

A matakan gwamnatocin jihohi, tsofaffin gwamnoni na samun irin wadannan kudi. Farfesan tsarin mulki, Nnamdi Aduba yana ganin hakan bai dace ba.

Kara karanta wannan

APC tayi waje da Minista, Tsohon Gwamna, da Wasu Daga kwamitin zaben Tinubu

Manyan lauyoyi irinsu Dr. Monday Ubani suna ganin biyan wadannan makudan kudi da ake yi ba zai taimaki tattalin arzikin Najeriya a irin yanzu ba.

Akpan Edet wanda Farfesa ne a fannin tattalin arziki yana ganin hakan facaka da dukiya ne, tamkar fashi a kasar da sauran ma’aikata ke cikin kunci.

Manufofin Bola Tinubu

Kuna da labari cewa alkawuran da ke kunshe cikin takardar manufofin ‘Dan takaran jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu sun hada da inganta tsaro.

Bola Tinubu ya yi alkawarin zai cigaba da bunkasa harkar noma, tare da kawo manufofin da za su inganta tattalin arzikin kasa da rage talauci a kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng