‘Dan Takaran PDP a Zaben 2023, Ya Cire Gabar Siyasa, Ya Yabi Shugaba Buhari

‘Dan Takaran PDP a Zaben 2023, Ya Cire Gabar Siyasa, Ya Yabi Shugaba Buhari

  • Peter Ndubuisi Mbah ya ji dadi da shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar da kamfanin man sa
  • Shugaban kasa da kan shi ya bude kamfanin Pinnacle Oil & Gas FZE a yankin Lekki a jihar Legas
  • Buhari ya yi murna da wannan kamfani, yace samunsa zai taimaka a wajen rage rashin aikin yi

Lagos - Peter Ndubuisi Mbah mai neman takarar Gwamnan jihar Enugu a karkashin inuwar jam’iyyar hamayya ta PDP a 2023 ya yabi Muhammadu Buhari.

‘Dan takarar gwamnan ya yabawa shugaban Najeriyan ne bayan ya kaddamar da tashar kamfaninsa na Pinnacle Oil & Gas FZE da ke garin Lekki a jihar Legas.

Mai girma Muhammadu Buhari yayin kaddamar da kamfanin yace zai taimaka wajen rage farashin mai, baya ga haka zai yi sanadiyyar samun ayyukan yi.

The Cable tace shugaban kasar yace kamfanin zai rage cunkoson da ake samu a tashar Apapa. Buhari ya fitar da jawabin da ya yi a kan shafinsa na Twitter.

Kara karanta wannan

2023: Kar Ku Yi Danasani da Mulkin Buhari, Tinubu Ga Yan Najeriya

Peter Mbah ya godewa shugaban kasa

Jim kadan bayan haka sai ga Peter Mbah yana jinjinawa shugaba Muhammadu Buhari na kaddamar da wannan kamfani da babu irin shi a saman teku.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Mbah ya yi magana a shafin Twitter, yake cewa a taya shi murna da cigaban da aka samu.

Muhammadu Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari Hoto: @PNMbah
Asali: Twitter

“Shugaba Muhammadu Buhari, ba za mu iya gode maka da kyau ba, da ka kasance tare da mu a yau. Mun gode da gudumuwa da karfafa gwiwa.”

- Peter Ndubuisi Mbah

Muhimmancin Pinnacle Oil and Gas Ltd

Ranar Asabar jaridar ta rahoto Mbah mai neman zama Gwamna yana cewa kamfaninsa mai karfin tara lita biliyan daya na mai zai bunkasa tattalin arziki.

Shugaban kamfanin na Pinnacle Oil and Gas Ltd yace suna tattaunawa da Dangote domin ganin yadda za a rika adana man da zai taimaki kasashen Afrika.

Kara karanta wannan

Goodluck Jonathan Ya Zama Dan Gudun Hijira, In Ji Gwamnan Bayelsa

Lauyan wanda ya koma neman kudi yanzu yace kamfaninsa yana da katafaren tankin da zai iya rike lita miliyan 300 na man fetur da dizil a lokaci daya.

Ana sa ran kamfanin Pinnacle Oil & Gas Ltd ya iya fitar da litoci miliyan 20 a kullum. Shiyasa shugaban kasa yace yana fatan ganin irin wadannan kamfanoni.

NNPC tana kashe Biliyoyi

Kuna da labari cewa Ma’aikatan NNPC sun lakume albashin N388.4bn a watanni 12, sannan sun kashe Naira Biliyan 15 a sayen katin wayan salula a 2021.

Binciken da aka gudanar ya nuna yadda Darektocin kamfanin NNPC suka tashi da kusan N400m, baya ga haka tafiye-tafiye ya ci N15bn a shekarar bara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng