2023: Kar Ku Yi Danasani da Mulkin Buhari, Tinubu Ga Yan Najeriya

2023: Kar Ku Yi Danasani da Mulkin Buhari, Tinubu Ga Yan Najeriya

  • Gabannin zaben 2023, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC ya bukaci yan Najeriya da kada su yi danasani da mulkin Buhari
  • Asiwaju Bola Tinubu ya nemi al'ummar kasar da su yi watsi da magauta da ke cewa shugaban kasar bai tabuka komai ba a shekaru bakwai da ya yi a mulki
  • Tsohon gwamnan na jihar Lagas ya ziyarci Kano inda ya kaddamar da ofishin yakin neman zabensa a jihar

Kano - Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya bukaci yan Najeriya da kada su yi danasani kan mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Tinubu ya ce kada su bari masu adawa su yaudare su cewa shugaban kasar bai tabuka komai ba tsawon shekaru bakwai da ya yi kan karagar mulki.

Kara karanta wannan

Karo na biyu, TY Danjuma Ya Yi Kira Ga Yan Najeriya Su Dau Bindigu Su Kare Kansu

Tinubu in Kano
2023: Kar Ku Yi Danasani da Mulkin Buhari, Tinubu Ga Yan Najeriya Hoto: @TheNationNews
Asali: Twitter

Tsohon gwamnan na jihar Lagas ya yi jawabi ne a Kano yayin kaddamar da ofishin yakin neman zaben shugaban kasa na APC a jihar.

Ya ce:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“Kada ku yi kowani danasani. Kada ku bari wadanda basu san hanyar nasara ba, wadanda basu fahimci nasarar kasa ba su yi maku karya game da Buhari ko wani. Kada ku basu dama. Ku mayar masu da martani. Ku rike tsintsiyarku da kyau sannan ku share Najeriya tsaf.
“Wannan jam’iyya za ta samu nasara, wannan kasar za ta samu ci gaba, wannan ofishin zai cika da farin ciki a Fabrairun 2023.
“Wadanda nake ganin ban basu tukwici yadda ya kamata ba, ina rokonku ku manta da hakan. Lokacin Allah shine mafi alkhairi. Allah zai amsa addu’o’inku sannan ya saka maku da alkhairi. Yanzu haka da nake tsaye a gabanku, na yi maku alkawarin cewa zan sauya tsarin bayar da tukwici na da zaran na zama shugaban kasa Insha Allah. Ba za ku yi danasanin yiwa jam’iyyarmu aiki ba.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Buhari Ya Sha Alwashin Yi wa Tinubu Gagarumin Kamfen

“Wannan abun farin ciki ne a gareni dawowa gida Kano. Ba za mu gudanar da kowani gangami ba, muna dubawa ne da tattaunawa da kungiyoyin yan kasuwa. Zan dawo idan na shirya yin babban gangami.”

Tinubu Ya Ware Makudan Miliyoyi, Ya Tallafawa Mutanen da Ambaliya Ta Shafa a Kano

A wani labarin, mun ji cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya bayar da tallafin naira miliyan 100 ga wadanda ambaliyar ruwa ta ritsa da su a Kano.

Nigerian Tribune ta rahoto cewa Tinubu ya sanar da bayar da tallafin ne a wajen taron cin abincin dare wanda kungiyar yan kasuwa ta Kano ta shirya masa a ranar Asabar.

Tinubu ya ce ya bayar da tallafin ne domin rage radadi ga wadanda lamarin ya ritsa da su a kananan hukumomin jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel