Tinubu Ya Bayyana Yan Takara Biyu Da Zasu Ba Shi Wahala a 2023, Ya Watsar da Kwankwaso
- Ɗan takarar shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, yace duk cikin yan takara, mutum uku ne fafatawa zata yi zafi a 2023
- Yayin ganawa da shugabannin ƙungiyar Tijjaniyya a Kano, Tinubu ya kira Atiku na PDP da mai yunkurin raba kawunan yan Najeriya
- Tsohon gwamnan Legas ɗin ya tsokaci kan batun wutar lantarki, inda ya ambaci makudan kudin da PDP ta kashe amma ba biyan bukata
Kano - Ɗan takarar shugaban kasa karƙashin inuwar jam'iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya tsayar da fafatawar zaɓen shugaban kasa a 2023 a tsakanin mutum uku kacal.
Jumullar jam'iyyun siyasa 18 ne suka tsayar da masu neman kujera lamba ɗaya a Najeriya, amma ɗan takarar jam'iyya mai mulki ya nuna cewa shi da 'yan takara biyu ne zasu gwabza a watan Fabrairu.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa a kalaman Tinubu ya nuna cewa Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP da Peter Obi na Labour Party ne kaɗai manyan 'yan takara.
Duk da bai ambaci sunayen sauran mutum biyu ba, amma abokin takararsa, Kashim Shettima, ya yi karin haske kan kalaman Tinubu yayin ganawa da Malaman Tijjaniyya a Kano ranar Lahadi.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Peter Obi ya kira jihar Legas gida ba Ekwulobia ko Awka ba saboda Tinubu ya gina jihar ta zama wurin zaman lafiya. Legas ce ta 5 mai girman tattalin arziki a Afirka," inji Shettima game da ɗan takarar LP.
Dangane da Atiku, yace, "Tinubu Ba zai raba lokacinsa kashi 50 a Dubai sauran kashi 50 a Najeriya ba."
Tinubu ya kira Atiku da, "Mai raba kawuna" ya kafa hujja da kalaman da ɗan takarar na PDP ya yi yayin tattaunawa da manyan Arewa a Arewa House dake Kaduna, Punch ta ruwaito.
Sauran mu uku ne a tseren kujera lamba ɗaya a Najeriya - Tinubu
"A baki ɗaya da muka shiga tseren, sauran mu uku kacal, ko ba haka bane? Ɗaya ya faɗi muhimmiyar jarabawa, kai mai haɗa kai ne ko me rabawa. Yace shi ɗan arewa ne," inji Tinubu.
Tsohon gwamnan jihar Legas ɗin ya yi tsokacin kan samar da wutar Lantarki, inda yace PDP ya kashe dala biliyan $16bn a shekara 16 amma ta gaza shawo kan lamarin.
A wani labarin kuma Atiku Ya Samu Gagarumin Goyon Baya, Ɗan Takarar Mataimakin Gwamna da Wasu Sun Koma PDP
Ɗan takarar mataimakin gwamna na jam'iyyar ADC a jihar Oyo, Emmanuel Oyewole, ya koma PDP.
Mista Oyewole yace gwamnatin Makinde ta yi abin a zo a gani a zangon farko, don haka ta cancanci zarcewa kan madafun iko.
Asali: Legit.ng