Ana Zargin Shugaban Jam’iyya Ya Dauki Mataki ba da Sanin Sauran Shugabannin APC ba

Ana Zargin Shugaban Jam’iyya Ya Dauki Mataki ba da Sanin Sauran Shugabannin APC ba

  • Bisa dukkan alamu Darektocin da aka dakatar daga aiki a sakatariyar jam’iyyar APC sun rasa kujerunsu
  • Tun a watan Afrilun 2022, shugaban APC na kasa ya umarci Darektocin APC su tafi hutun tsawon kwana 30
  • Duk da hutun ya kare a Watan Mayu, ba su dawo ofis ba, ana zargin Abdullahi Adamu ya maye gurabensu

Abuja - Ana samun sabani a jam’iyyar APC na kasa yayin da aka ji Abdullahi Adamu ya maye gurbin Darektocin da ya dakatar daga aiki kwanakin baya.

Daily Trust tace Sanata Abdullahi Adamu ya nada sababbin Darektoci a duka sassan jam’iyya da za su canji wadanda aka sauke a kan zargin rashin gaskiya.

Darektocin da aka yi waje da su su ne Elder Anietie Offong (Walwala da jin dadi); Bartholomew I. Ugwoke (Bincike); da kuma Abubakar Suleiman (Kudi).

Kara karanta wannan

Wasu Shugabannin PDP na Neman Tada Rikici, Sun ce An Ware Su a Yakin Zaben Atiku

Sauran darektocin da aka canza sun hada da Dr. Suleiman Abubakar (Gudanarwa); Salisu Na’inna Dambatta (Yada labarai); da kuma Dare Oketade (shari’a).

Aikin kwamitin Ali Saad Birnin Kudu

Bayan Adamu ya karbi rikon APC, ya nada kwamiti a karkashin jagorancin tsohon Gwamnan Jigawa, Ali Saad Birnin Kudu ya nuna masa inda zai fara aiki.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ali Saad Birnin Kudu ne ya duba takardun da kwamitin Mai Mala Buni ya bari a game da rikicin cikin jam’iyya, ya kuma bada shawarar canza Darektoci.

Shugabannin APC
Shugabanni da Jagororin Jam'iyyar APC Hoto: @OfficialAPCNg
Asali: Twitter

Kwamiti na rikon kwarya ya ba uwar jam’iyya shawarar canza darektocin, haka kuma aka yi.

Adamu ya amince a dakatar da su duk da sun yi ta kokarin su dawo kan kujerunsu ta hanyar aikawa majalisar NEC ta jam’iyya takarda, amma abin ya gagara.

Rahoton yace daga baya wadannan darektoci da suka rasa mukamasu sun rubuta wasiku zuwa ga majalisar NWC da kungiyar gwamnonin APC watau PGF.

Kara karanta wannan

Rashin Lafiya Ya Jawo Aka Gaggauta Fita da Atiku Kasar Waje - 'Dan Kwamitin Zaben APC

An kawo wasu sababbin Darektoci

A watan Mayun 2022 ne wa’adin dakatar da su daga ofis da aka yi ya cika, amma har yau ba a bari sun koma kan mukamansu ba, ana zargin an maye gurbinsu.

Wata majiya ta shaidawa jaridar cewa Adamu da sakatarensa, Sanata Iyiola Omisore sun kawo sababbin darektoci ba tare da sauran ‘Ya 'yan NWC sun sani ba.

An tuntubi wani Hadimin shugaban APC na kasa da kakakin jam’iyya, Felix Morka domin jin ta bakinsu, amma ba su tanka ‘yan jarida ko sun yi karin bayani ba.

Mustapha Inuwa da Siyasar Katsina

Kun samu rahoto cewa akwai yiwuwar Mustapha Muhammad Inuwa ya nakasa jam’iyyar APC a Jihar Katsina da komawarsa PDP da ya yi a makon nan.

Tsohon malamin jami'ar yana cikin kusoshin APC a Katsina kafin ya canza sheka. Shi da mutanensa za su taimakawa 'dan takaran PDP, Lado Danmarke.

Kara karanta wannan

2023: Dalilin Da Zai Sa In Zabi Peter Obi Matsayin Shugaban Kasa, Sheikh Gumi

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng