Yadda Sauya shekar Tsohon SSG Za ta Iya Birkita Lissafin Jam’iyyar APC a Katsina

Yadda Sauya shekar Tsohon SSG Za ta Iya Birkita Lissafin Jam’iyyar APC a Katsina

  • Zaman Mustapha Muhammad Inuwa a jam’iyya mai mulki ya kare bayan komawarsa PDP kwanan nan
  • Ficewar tsohon Sakataren gwamnatin na Katsina daga APC zai iya taimakawa PDP a zaben Gwamnan Jiha
  • Wasu daga cikin mutanen Mustapha Inuwa za suyi wa Sanata Lado Danmarke da Jam'iyyar PDP aiki a 2023

Katsina -Mustapha Muhammad Inuwa ya sauya-sheka zuwa PDP a makon nan. Daily Trust tace wannan mataki zai iya canza lissafin siyasar Katsina.

Kafin zamansa Sakataren gwamnatin jiha, ‘dan siyasar ya rike Kwamishinan harkar ilmi da shugaban hukumar KSTA tsakanin 1999 zuwa Mayun 2007.

Daga baya ya jagoranci APC a lokacin tana jam’iyyar hamayya, kafin ta kafa gwamnati a 2015. Daga nan ya dare kujerar SSG na shekaru bakwai.

Kara karanta wannan

Adamawa 2023: Jam'iyyar APC Ta Maida Martani Mai Zafi Kan Hukuncin Soke Tikitin Gwamnan Aishatu Binani

Inuwa ya fice daga APC ne bayan zamansa a jam’iyyar ya gagara a sakamakon nasarar Dr. Dikko Umar Radda a zaben ‘dan takarar Gwamnan 2023.

Jam’iyyar PDP za ta iya komawa gidan gwamnatin Katsina kamar yadda masu fashin-bakin siyasa ke hasashe, Lado Danmarke yake takarar a 2023.

PDP tayi karfi a jihar Katsina kuma ita ta rika cin zabe daga 1999 zuwa 2015, duk da nan ne mahaifar Mai girma shugaban kasa mai-ci, Muhammadu Buhari.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Tsohon jigon Jam’iyyar APC a Katsina
Tsohon jigon Jam’iyyar APC a Katsina, Mustapha Muhammad Inuwa Hoto: Mallam Abdul Danja
Asali: Facebook

Masu nazarin siyasar Katsina sun shaidawa jaridar ficewar Inuwa daga APC zai kawowa jam’iyyar cikas idan aka yi la’akari da wadanda ke tare da shi.

A cikin shugabannin PDP na reshen jiha, ana zargin irinsu tsohon shugaban jam’iyya watau Sabiu Shitu Sabiu suna tare da Mustapha Inuwa a tafiyar siyasa.

Abin da ake tsoro shi ne tsohon sakataren gwamnatin ya kafa mutane da-dama a jam’iyya mai mulki, kuma ‘yan takarar kujeru da yawa suna tare da shi.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Wike Ya Dauki Ortom, Makinde Da Ikpeazu Sun Shilla Kasar Waje, An Bayyana Dalilin Fitarsu

Ratar da ke tsakanin tsohon sakataren gwamnatin da tsohon shugaban na SMEDAN a zaben tsaida gwani bai da yawa, Inuwa yana zargin kudi ne ya yi tasiri.

Dikko Umar Radda ya dage da kamfe

Legit.ng Hausa ta fahimci a gefe guda, Dr. Dikko Radda mai neman takara a APC wanda kafin yanzu bai kai Inuwa karfi a siyasar APC da jihar ba, ya ja daga.

Gwamna Aminu Bello Masari yana kokarin hada-kan ‘ya ‘yan APC su goyi bayan tsohon shugaban ma’aikatan fadarsa domin ya doke Danmarke a zaben badi.

Inuwa ya koma PDP

An samu rahoto cewa mutumin da ya fi kowa dadewa a kan kujerar Sakataren gwamatin jihar Katsina, Mustapha Muhammad Inuwa ya bar jam’iyyar APC.

Inuwa ya dauki wannan matsaya ne bayan ya gana da daruruwan magoya bayansa da kungiyoyin masoya da ke ganin shi ne gwarzon siyasa a jihar ta Katsina.

Asali: Legit.ng

Online view pixel