Tinubu, Obi Ko Atiku? Gwamna Wike Ya Fadi Irin Dan Takarar da Ya Kamata Kowa Ya Zaba a 2023

Tinubu, Obi Ko Atiku? Gwamna Wike Ya Fadi Irin Dan Takarar da Ya Kamata Kowa Ya Zaba a 2023

  • Gwamnan jihar Ribas ya bayyana shawarinsa ga 'yan Najeriya kan batun irin shugaban da zasu zaba a zaben 2023
  • Nyesom Wike, ya bayyana hakan ne a jihar Legas yayin da halarci wani taron mata da aka yi a jihar Legas
  • Gwamna Wike na ci gaba da kai ruwa rana tare da bude aiki ga 'yan PDP da, ciki har da dan takarar shugaban kasansu

Jihar Legas - Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya yi magana game da irin dan takarar da zai marawa baya a zaben 2023 mai zuwa.

Gwamnan dake kai ruwa rana da Atiku ya bayyana cewa, Najeriya na bukatar shugaban da zai kare muradan 'yan kasa baki daya ne ba wai wata kabila ba.

Kara karanta wannan

Rashin Lafiya Ya Jawo Aka Gaggauta Fita da Atiku Kasar Waje - 'Dan Kwamitin Zaben APC

Ya ce, don haka wanda zai marawa baya dole ya kasance 'yan Najeriya a zuciyarsa, kuma zai yi aiki tukuru.

Gwamna Wike ya bayyana irin shugaban da zai marawa baya
Tinubu, Obi Ko Atiku? Gwamna Wike Ya Fadi Irin Dan Takarar da Ya Kamata Kowa Ya Zaba a 2023 | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Wike ya bayyana matsayarsa ne a ranar Talata 18 ga watan Oktoba a yayin bude wani taron mata da aka gudanar a jihar Legas, Channels Tv ta ruwaito.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

2023: Bai kamata 'yan Najeriya su zabi dan takara mara gogewa ba, inji Wike

Da yake magana game da kwarewar 'yan takara, gwamnan ya ce, kamata ya yi 'yan Najeriya su yi layi domin zaban shugaba mai gogewa a fannin shugabanci.

Hakazalila, ya ce ya kamata su duba wanda ya san lungu da sako na yadda zai magance matsalar tattalin arziki da rashin tsaro idan aka zabe shi.

A cewar Wike:

"Muna neman shugaban kasan da yake da kwarewa da gogewa a shugabanci, wanda zai sanya abinci a gaban kowa kuma ya yaki rashin tsaro.

Kara karanta wannan

Ku Zabi Tinubu Zai Kare Muradun Arewacin Najeriya, Sanata Abu Ibrahim

"Wannan shine mutumin da muke bukata; ba wasu mutane dake maganar kabilanci ba."

Ya zuwa yanzu, gwamna Wike na ci gaba da kai ruwa rana da Atiku da sauran jiga-jigan PDP kan matsayarsa na a tsige shugaban PDP, Iyochia Ayu.

Saboda Barin Baya Mai Kyau, Na Yi Ayyuka Masu Tasiri Barkatai

A wani labarin, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yaba da irin ayyukan da gwamnatinsa ta yi masu tasiri a bangarori daban-daban na kasar nan, jaridar TheCable ta ruwaito.

Shugaban ya bayyana hakan ne a lokacin da yake magana a taron waiwaye ga ayyukan ministocinsa da aka shirya don duba makomar ajandoji tara na gwamnatinsa.

Da yake magana a taron a ranar Litinin, Buhari ya bayyana kadan daga nasarorin da gwamnatinsa ta samu a fannin ayyukan more rayuwa, noma, tattalin arziki da lafiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel