Da Dumi-Dumi: Wasu Sabbin Hotuna Daga Aso Villa Sun Nuna Tinubu Na Kus-Kus da Mataimakin Buhari
- Jam'iyyun siyasa na ta kokarin ganin sun hada kan 'ya'yansu yayin da guguwar zaben 2023 ke kara kadowa
- Ga dukkan alamu, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, yana buga wasansa yadda ya dace
- A ranar Talata, 18 ga watan Oktoba ne aka gano shi tare da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo suna kuskus a villa
Abuja – Gabannin babban zaben 2023, wasu hotuna sun bayyana na mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo da dan takarar shugaban kasa na APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, a ranar Talata, 18 ga watan Oktoba.
An gano jiga-jigan jam’iyyar mai mulki a tare yayin da suka halarci taron ministocin gwamnatin Buhari a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Hotunan da aka gabatarwa jaridar Legit.ng sun isa shaida cewa shugabannin biyu na ci gaba da huldarsu kamar yadda suka saba.
Daga kallon abubuwa, mutum na iya hararo cewa idan ba don shawarar da dan takarar na APC ya yanke na zabar Musulmi a matsayin abokin takara ba ko shakka babu da za su yi aiki tare a babban zaben 2023 mai zuwa.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Sanatan Kano Ya Bayyana Ainahin Wanda Osinbajo Yake Goyon Baya A Zaben Shugaban Kasa Na 2023
A wani labarin, Sanata Kabiru Gaya ya tabbatar da cewar dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, da mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo suna aiki kai da fata.
Sanatan ya ce bayan Tinubu ya bayyana a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar mai mulki, ya ziyarci Osinbajo a gidansa sannan ya nemi ya goya masa baya.
Daily Trust ta rahoto cewa Sanata Gaya ya kara da cewa sabanin rade-radin da ke yawo, ba a mayar da mataimakin shugaban kasar saniyar ware ba a wajen kafa tawagar yakin neman zaben takarar shugabancin APC.
Asali: Legit.ng