INEC Ta Damu Matuka da Rikicin da Ake Samu a Wuraren Yakin Neman Zabe, Ta Gargadi Jam’iyyu
- Hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta bayyana kadan daga tsoron da take ciki tun bayan fara gangamin kamfen a Najeriya
- Jam'iyyun siyasa na ci gaba da rikici da juna, lamarin da ka iya kaiwa ga zubar da jini idan ba a samar da mafita ba
- Lokatan kamfen a Najeriya na zuwa da sauyin yanayi, inda magoya bayan jam'iyyu ke ruwa da tsaki don tallata 'yan takararsu a sassan kasar
FCT, Abuja - Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta bayyana kaduwa da damuwa game da abubuwan dake faruwa na rikici tsakanin jami'iyyun siyasa a fadin kasar nan.
Hukumar ya damuwa da yadda magoya bayan jam'iyyun siyasa ke yin kare jini biri jini a lokutan da suke yawon gangami a Najeriya, rahoton Punch.
Shugaban INEC, Mahmood Yakubu ya bayyana kokensa ne a ranar Talata 18 ga watan Oktoba a wani taron horarwa na fasaha da hukumar ta gudanar kan zaben 2023.
A cewarsa:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Musabbabin rikici tsakanin jam'iyyun siyasa da magoya bayansu a wasu jihohin kasar nan a lokutan gangamin kamfen babban abin damuwa ne.
“Haka nan, akwai barazanar hana jam’iyyu da ’yan takara shiga wasu wurare mallakin gwamnati a wasu jihohin tarayyar kasar nan.
"Ina gargadin jam'iyyun siyasa da magoya bayansu da su mai da hankali ga lamuransu kuma su guje takalar juna."
A bangare guda, ya ce hukumar za ta ci gaba sa ido don tabbatar da an gudanar kamfen cikin kwanciyar hankali, har da zabukan da za a gudanar a shekara mai zuwa, inji rahoton BusinessDay.
Gwamna El-Rufai Ya Tuna da Irin Rashin Mutuncin da Peter Obi Ya Yi Masa a 2013
A wani labarin, gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai ya bayyana a wani faifan bidiyon da TVC ta yada, inda yake bayyana kadan daga abu mara dadi da tsohon gwamnan Anambra, Peter Obi ya yi masa.
Ya tuna cewa, a shekarar 2013, ya kai ziyarar duba zabe a jihar Anambra, a nan ne dai Obi ya tsare shi tare da kokarin tozarta shi saboda a lokacin baya rike da mukamin gwamna.
A cewarsa, yanzu kuma shine gwamna a jihar Kaduna, gashi kuma Peter Obi, wanda a yanzu dan takarar shugaban kasa ne a jam'iyyar Labour zai shigo jiharsa, amma ba zai masa komai ba saboda shi wayayye ne kuma mai sanin ya kamata, cikakken dan Arewa.
Asali: Legit.ng