Ba Mu da Wani 'Dan takara a Ran Mu - Kwamitin Arewa Ya Fadawa Kwankwaso
- Dr. Hakeem-Baba Ahmad ya yi bayani a kan zaman da manyan Arewa suke yi da ‘yan takaran 2023
- Dattijon yace kwamitin hadakan kungiyoyin Arewa ba zai yi wani son kai ko ya cutar da al’umma ba
- Baba Ahmad yace za suyi zama da masu neman mulki ne domin suyi masu baja-kolin manufofinsu
Kaduna - Kwamitin hadaka na kungiyoyin Arewa da za iyi zama da ‘yan takarar shugaban kasa ya karyata zargin da wasu suke yi masa na son-kai.
Ana zargin kwamitin da boyayyar manufar amfani da sunan Arewa domin tallata wani, Hakeem-Baba Ahmad ya yi a karin haske a game da lamarin.
Da yake bayani a shafinsa na Facebook, ya bayyana cewa Kwamitin hadakan na su bai da nufin saida takarar wani daga cikin masu neman mulki a 2023.
Baba-Ahmed Ya Gargadi Yan Najeriya Akan Su Guje Wa Yan Takara Masu Nuna Kabilanci da Addini a Zaben 2023
Dadin-dadawa, dattijon ya bayyana cewa suna maraba da wadanda suka kawo kansu, kuma ba su fushi da ‘dan takaran da ya kauracewa zama da su.
Aikin da kwamitin zai yi a kan zaben 2023
Dr. Baba Ahmad wanda shi ne kakakin kungiyar NEF yace manufar kwamitinsu shi ne kowane ‘dan takarar shugaban kasa ya fito masu da irin manufofinsa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A karshen jawabinsa, dattijon yace yana da kyau jama’a su gane cewa akwai mutane masu kima da daraja da sun karfin wani ‘dan siyasa ya yi amfani da su.
Jawabin yace kwamitin ba zai aikata wani abin da zai cutar da yankin Arewa saboda son kai ba.
“Kwamitin hadaka na kungiyoyin Arewa wanda yake zama a Kaduna da ‘yan takarar shugaban kasa a bainar jamaa, ba na sayarwa ba ne.
Ba shi da niyyar fifita wani dan takara. Ba shi da wata boyayyar niyya. Yana maraba da wanda yazo, kuma baya fushi da wanda bai zo ba.
Cewa muka yi kowa ya zo ya baje kolin sa.Idan wani ya ce shi ba zai yi ba, ba matsala, shi da jama’a.
Yana da kyau ‘yan Nigeria su fahimci cewa akwai mutane da yawa wadanda ba’a iya siyar su, ko a sa su suyi abin da zai cuci Arewa da jamaar Najeriya.”
Martani ga Kwankwaso?
Za a iya cewa wannan raddi ne ga Rabiu Kwankwaso wanda ya aikawa kwamitin doguwar wasika, yana mai zarginta da neman tallata wani ‘dan takara.
Kun ji labari ‘Dan takarar shugabancin na Najeriya ya zargi kwamitin da neman fifita wani ‘dan takara wanda bai shahara ba a kan mutanen Arewa a 2023.
Kwankwaso mai neman a mulki jam’iyyar NNPP ya yi kira ga manyan yankin su guji son kai.
Asali: Legit.ng