2023: Bola Tinubu Ya Bukaci Atiku Ya Janye Daga Takarar Shugaban Kasa Ya Mara Masa Baya
- Ɗan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Bola Tinubu, ya nemi Atiku Abubakar ya janye daga takara a 2023
- Tsohon gwamnan Legas ɗin ya bukaci Atiku ya saka masa da karamci ta hanyar aje tikitin PDP, ya mara masa baya
- A ranar Litinin, Bola Tinubu ya gana da shugabannin arewa a gidan tarin Arewa dake Kaduna kan tanadinsa ga yankin
Kaduna - Ɗan takarar shugaban kasa a inuwar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya nemi abokin fafatawarsa, Atiku Abubakar, ya janye daga takara kana ya mara masa baya gabanin babban zaben 2023.
Tinubu ya bukaci Atiku ya saka masa kan karamcin da ya masa lokacin da ya nemi takarar shugaban kasa a zaɓen 2007 karkashin inuwar jam'iyyar ACN ta hanyar janye wa kuma ya goya masa baya.
Tsohon gwamnan Legas ɗin ya yi wannan furucin ne a wurin taronsa da jagorocin arewacin Najeriya karkashin Kwamitin gamayyar kungiyoyin arewa, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.
2023: Atiku Ya Yi Martani Kan Harin Wasu 'Yan Daba a Wurin Kamfe Ɗinsa a Kaduna, Ya Tura Sako Ga Buhari
Taron dai na ɗaya daga cikin yunkurin shugabannin arewa na zauna wa da wasu 'yan takarar shugaban kasa domin tattauna wa da su kan tanadin da suka wa arewa gabanin zuwan zaɓen 2023.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A ruwayar Vanguard, Tinubu Yace:
"Na goyi bayan Atiku a 2007, kar ku ga laifi na idan na nemi a saka mun, ya dawo ya goya mun baya maimakon zuwa yana gudanar da gangami a Kaduna yayin da nake nan tare da ku."
Tinubu na APC ya gana da jagoron arewa ne kwanaki biyu bayan abokin hamayyarsa na jam'iyyar PDP ya yi makamancin wannan taro da su a Kaduna.
Su wa suka ɗauki nauyin wannan taro?
Legit.ng Hausa ta gano cewa zaman tattauna wa da juna wanda ya gudana a gidan tarihin arewa watau Arewa House gamayyar ƙungiyoyin arewa shida ne suka shirya.
Ƙungiyoyin sun hada da ƙungiyar tuntuba ta arewa, gidauniyar tuna wa da Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato, ƙungiyar dattawan arewa, Jama'ar matan arewa da sauransu.
A wani labarin kuma Gwamna Wike Yace ya zama wajibi PDP Ta fito ta baiwa yan Najeriya hakuri kan kalaman da Atiku ya yi
Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya nuna rashin jin dadinsa kan kalaman da dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar yayi.
Atiku ya ce dan arewa baya bukatar Bayarabe ko Inyamuri a matsayin shugaban kasa face wani dan arewa.
Asali: Legit.ng