Tinubu Ya Gaji, Kamata Yayi Ya Koma Gida Ya Yi Hutawarsa, Inji Na Hannun Daman Atiku

Tinubu Ya Gaji, Kamata Yayi Ya Koma Gida Ya Yi Hutawarsa, Inji Na Hannun Daman Atiku

  • Mai magana da yawun Atiku Abubakar, Phrank Shaibu ya bayyana Bola Tinubu a matsayin wanda bai cancaci zama shugaban kasa ba
  • Shaibu ya bayyana hakan ne bayan wata kwabsawa da Tinubu ya yi a wani taron da aka gudanar a jihar Kaduna
  • Dan takarar shugaban kasa na APC ya yi tsokaci game da ayyukan gwamna Nasir El-Rufai, ya ce ya 'sauya rubabbun lamurra zuwa munana'

FCT, Abuja - Jigon jam'iyyar PDP Phrank Shaibu ya caccaki dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu.

A wata sanarwa da ya aikewa Legit.ng a jiya Lahadi 16 ga watan Oktoba, Shaibu ya bayyana cewa, duba da lafiyar Tinubu, bai cancanci ya gaji shugaban kasa Buhari ba.

Jigon PDP ya ce Tinubu ya gaji, ya kamata ya koma gida ya huta
Tinubu Ya Gaji, Kamata Ya Yi Ya Koma Gida Ya Yi Hutawarsa, Inji Na Hannun Daman Atiku | Hoto: vanguardngr.com
Asali: Facebook

Ya kuma bayyana cewa, Tinubu ya sha kwabsawa a maganganunsa tun bayan da ayyana aniyarsa ta zama shugaban kasa, wanda hakan ke nuna a rude yake gaba daya.

Kara karanta wannan

Da Dumi-dumi: Dole PDP Ta Fito Ta Baiwa Yan Najeriya Hakuri Kan Maganganun Atiku - Wike

Tinubu a rude yake, kuma bai da lafiya, inji hadimin Atiku

Shaibu, wanda kuma shine mai magana da yawun dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya ce maganar Tinubu ta baya-bayan nan a Kaduna ta sake nuna rudewar Tinubu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa:

"Tinubu ya gaji, ya kamata ya tafi gida ya huta.
"Idan kuka kalli dan takarar shugaban kasan APC, za ku ga mutumin da ya gaji kuma mai rauni. Kuma kun sha jin irin kwabsin da ya sha fitowa daga gare shi tun ma kafin ya fara gangamin kamfen."

Najeriya na bukatar mai jini a jika, bayanin Phrank

Ya kara da cewa:

"Najeriya a yanzu na cikin wani irin mawucin yanayi da a kowane fanni na tattalin arziki na cikin cakwalkwali; don haka, kasar nan ba zai yiwu ta koma karkashin shugaban kasa mara lafiya ba."

Kara karanta wannan

Allah zai kama mu idan bamu goyi bayan Tinubu ba, inji shugaban kungiyar CAN

Ya kuma tunawa 'yan Najeriya cewa, a ranar Labara, 8 ga watan Yuni, kadan ya hana Tinubu ya fadi a lokacin da yake magana a Eagle Sqaure, inda aka yi taron gangamin APC.

Ya kuma bayyana cewa, yayin da Tinubu ke magana a taron gangamin, an ga hannayensa na rawa, lamarin dake nuna akwai alamar tambaya ga lafiyarsa.

Atiku ya kamata a zaba, inji jigon APC

Ya kara da cewa:

"Kasar nan na bukatar shugaban da ya cancanta. Ofishin shugaban kasa ba na mutum mara lafiya bane. Tinubu yi iyakar kokarinsa amma dai yanzu ya gaji kuma ya kamata ya koma gida domin ya cancanci ya huta."

Hakazalika, ya bayyana damuwar cewa, a nahiyar Afrika ne kawai ake samun mara lafiya amma ya dage sai ya dale kujerar shugabanci, duk kuwa irin matsalar tattalin arzikin da kasa ke fuskanta.

Daga karshe ya shawarci masu kada kuri'u da su zabi Atiku, tare da cewa, shi kadi ne zai iya daidaita kasar nan.

Kara karanta wannan

Lamari Ya Dagule Bayan Atiku Yace Arewa Bata Bukatar Bayerabe Ko Ibo Ya Mulki Najeriya a 2023

Allah Sai Ya Tambaye Mu Idan Bamu Zabi Dan Takarar APC Tinubu Ba, Inji Kungiyar CAN Ta Legas

A wani labarin kuma, shugabancin kungiyar kiristoci ta Najeriya (CAN) reshen jihar Legas ta bayyana goyon bayanta ga dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmad Tinubu.

Wannan batu na goyon baya na fitowa ne a ranar Lahadi, 16 ga watan Oktoba daga bakin shugaban CAN na Legas, Rabaran Stephen Adegbite, inji rahoton jaridar Independent.

A nasa fahimtar, shugaban na CAN ya ce, tabbas Allah zai hukunta duk wani kirista a karkashin CAN ta Legas da ya ki goyon bayan Tinubu a zabe mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.