Jerin Jihohin da a Za a Kai Ruwa Rana a Zaben Gwamnan 2023 Mai Zuwa
- Za a samu zabuka masu kama da 'kare jini biri jini' a zaben gwamnan 2023 a jihohi 17 a Najeriya saboda gwamnonin jihohin masu barin kujera ne bayan wa'adi na biyu
- Wasu daga cikin gwamnonin, sun yi ruwa sun yi tsaki wajen ganin 'yan takarar da suke so ne za su gaje su a zaben mai zuwa
- Alal misali, gwamna Ifeanyi Okowa, ya yi ruwa da tsaki wajen toshe burin James Ibori wajen zabo dan takara, ya tabbatar PDP ta zabo wanda yake so a matsayin dan takarar gwamna
Akalla a jihohi 17 ne cikin 28 za a iya samun zaben gwamna mai tsauri a 2023 kasancewar gwamnoni masu ci a jihohin ka iya aiki tukuru don ganin sun daura 'yan takarar da suke so su gaje su.
Gwamnoni 17 ne a Najeriya suke kan wa'adi na biyu na mulki, kuma daidai da ka'idar INEC, za su sauka a zaben 2023 don daura sabbin masu jan ragama a jihohinsu.
2023: Wike Da Wasu Gwamnoni 4 Da Suke Fushi Da PDP Sun Hada Kai Da Tinubu, Ortom Ya Rungumi Peter Obi
Sabon batu game da zaben gwamnoni na 2023
Abu ne a bayyane, wasu gwamnoni ka iya kokari wajen kawo magajin da suka zaba suke so domin ci gaba daga inda suka tsaya.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Jerin 'yan takarar da hukumar zabe mai zaman kanta, INEC ta fitar ya sa 'kallo sama' tsakanin gwamnonin 17 da sauran 'yan takara.
A cewar jerin na INEC, jam'iyyun siyasa 18 ne ke da 'yan takara 837 na zaben gwamna a jihohi 28 yayin da aka samu 'yan takara 10,231 ne ke neman kujeru 993 na majalisun jihohi a fadin kasar nan.
Karshen wa'adi na biyu: Jerin jihohin da gwamnoninsu za su sauka a zabe mai zuwa
- Abia - Okezie Ikpeazu
- Rivers - Nyesom Wike
- Cross River - Ben Ayade
- Udom Emmanuel - Akwa Ibom
- Delta - Ifeanyi Okowa
- Enugu - Ifeanyi Ugwuanyi
- Ebonyi - Dave Umahi
- Katsina - Aminu Masari
- Benue - Samuel Ortom
- Kaduna - Nasir El-Rufai
- Kano - Umar Ganduje
- Sokoto - Aminu Tambuwal
- Niger - Abubakar Sani Bello
- Jigawa - Abubakar Badaru
- Taraba - Dairus Ishaku
- Kebbi - Atiku Bagudu
- Plateau - Simon Lalong
Dalilin da yasa zabe zai zama mai tsauri a wasu jihohin
Hakazalika, akwai jihohin da zabe zai yi dumi saboda gwamnoni masu barin gado sun yi fama da iyayen gidajensu na siyasa a zabukan fidda gwani da kuma fafutukar neman magaji.
A jiha kamar Delta, gwamna Okowa da uban siyasa James Ibori sun kai ruwa rana a lokacin zaben fidda gwanin da aka gudanar.
Okowa, wanda shine abokin takarar Atiku ya goyi bayan Sheriff Oborevwori a zaben fidda gwanin gwamnan da aka gudanar a Delta.
Hakazalika, gwamnoni Ugwuanyi da Ikpeazu sun yi ruwa da tsaki wajen ganin sun dasa 'yan takarar da suke so a jihohinsu.
Gwamnatin Tarayya Kadai Ba Za Ta Iya Rike Jami'o'i Ba, Iyaye Ya Kamata Su Fara Tallafawa, Inji Gwamna Inuwa
A wani labarin, gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya na jihar Gombe ya bayyana cewa, gwamnatin tarayya kadai ba ta da karfin iya rike jami'o'in kasar, Channels Tv ta ruwaito.
Ya kuma bayyana cewa, akwai bukatar iyaye da sauran masu ruwa da tsaki suke shiga lamarin domin tabbatar da tafiyar da makarantu cikin kwanciyar hankali.
Gwamnan ya bayyana hakan a ranar Juma'a jim kadan bayan da kungiyar ASUU ta ayyana janye yajin aikin da ta shafe watanni takwasi tana yi a kasar.
Asali: Legit.ng