Yan Bindiga Sun Halaka Shugaban Matasan APC, Sun Sace Wasu 5 a Ebonyi

Yan Bindiga Sun Halaka Shugaban Matasan APC, Sun Sace Wasu 5 a Ebonyi

  • Wasu mahara sun bindige shugaban matasan APC har lahira a gundumar Obegu, karamar hukumar Ishielu jihar Ebonyi
  • Wata majiya tace maharan sun kuma yi garkuwa da wasu mutum biyar da suka zo wucewa ba tare da sanin abinda ke wakana ba
  • Shugaban karamar hukumar ya musanta raɗe-raɗin Fulani ne suka kai harin, yace lamarin na da alaƙa da siyasa

Ebonyi - Shugaban matasan jam'iyyar APC na gundumar Obegu ƙaramar hukumar Ishielu, jihar Ebonyi, Hon Celestine Egbuaba, ya mutu a wani hari mai alaƙa da siyasa.

Wata majiya ta shaida wa Leadership bisa sharaɗin boye bayananta cewa wasu yan bindiga kusan 10 daga kauyen shugaban matasan ne suka tare shi, kana suka halaka shi.

A cewar majiyar, maharan sun kuma farmaki masu wucewa waɗanda suka dawo daga gonakinsu ko wurin kasuwanci suka faɗa wa yan bindigan ba tare da sani ba.

Kara karanta wannan

Abinda Yasa Nake Da Gwarin Guiwar Cewa Ni Zan Lashe Zaben Shugaban Kasa a 2023, Tinubu Ya Magantu

Harin yan bindiga.
Yan Bindiga Sun Halaka Shugaban Matasan APC, Sun Sace Wasu 5 a Ebonyi Hoto: leadership.ng
Asali: Twitter

Majiyar, wata dattijuwar mata da ta dawo gona amma ta yi hanzarin ɓuya a Jeji, tace duk da magiyar da shugaban matasan ya musu, sai da maharan suka harbe shi a ciki lokacin da ya yi yunkurin guduwa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ta ƙara da cewa jim kaɗan bayan kashe jigon APC, yan bindigan suka yi awon gaba da sauran mutanen zuwa cikin jeji.

"Ina hanyar dawowa daga gona sai naji maganganu cikin sauri na ɓuya a cikin duhuwar daji ta yadda ina hangen abinda ke faruwa. Maharan sun kama shugaban matasan suna bincikarsa kudin tallafin da ya karba kwanan nan."
"Shugaban matasan ya roki kar su raba shi da rayuwarsa amma duk magiyarsa a banza ɗayansu ya ba da umarnin su sheƙe shi. Nan suka harbe shi suka bar shi cikin jini suka tsere cikin jeji."

Kara karanta wannan

Yadda Zan Tsaya Na Yaki Yan Bindiga Idan Na Zama Shugaban Kasa a 2023, Tinubu

- Inji matar.

Majiyar ta kara da cewa wasu mutane da suka faɗa musu ba tare da sanin abinda ke aukuwa ba harin ya rutsa da su, wasu sun jikkata yayin da wasu suka tsallake rijiya da baya.

Su wa suka kai harin?

Da yake tabbatar da aukuwar lamarin, shugaban karamar hukumar, Hon Obinna Onwe, ya musanta rahoton da wasu ke taɗa wa cewa Fulani Makiyaya ne suka kai harin.

Yace kisan ba zai rasa alaƙa da siyasa ba, inda ya kara da cewa bayan kashe shugaban matasan, yan bindigan sun kira shugaban APC na gundumar Obegu suka yi masa barazana.

Ya bayyana cewa daga cikin waɗanda maharan suka yi garkuwa da su a harin harda wani shugaba, "Nan ba da jima wa ba jami'an tsaro zasu kamo maharan tare da gano maƙasudin harin."

A wani labarin kuma Bayanai Sun Fito Kan Rahoton Dake Yawo Wasu Matasa Sun Farmaki Ayarin Bola Tinubu Na APC

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Ɗan Fitaccen Ɗan Majalisar Arewa, Sun Kashe Jami'in Tsaro

Hukumar yan sandan jihar Osun ta musanta wani rahoto da ake yaɗa cewa cewa wasu matasa sun farmaki Bola Ahmed Tinubu.

Kwamishinan yan sandan jihar, Olawale Olokode, yace Bidiyon da ake yaɗa ba na yanzu bane.

Asali: Legit.ng

Online view pixel