Sanusi II ya Sanar da Tinubu Cewa Bashi da Jam’iyyar Siyasa, Najeriya ce a Gabansa

Sanusi II ya Sanar da Tinubu Cewa Bashi da Jam’iyyar Siyasa, Najeriya ce a Gabansa

  • Khalifa Muhammad Sanusi II, tsohon Sarkin Kano kuma tsohon Gwamnan babban bankin Najeriya yace bashi da jam’iyyar siyasa a Najeriya
  • A bayanin da yayi gaban ‘Dan takarar kujerar shugabancin kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, yace Najeriya ce jam’iyyarsa
  • Sanusi II ya jajanta matsalolin tattalin arziki da Najeriya ke fama da su da suka hada da satar man fetur, taruwar bashi, tallafin mai da lalacewar kudin kasar

Tsohon Gwamnan babban bankin Najeriya, Sanusi Lamido Sanusi a ranar Asabar, ya sanar da ‘Dan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu cewa bashi da jam’iyyar siyasa.

Khalifa Sanusi
Sanusi II ya Sanar da Tinubu Cewa Bashi da Jam’iyyar Siyasa, Najeriya ce a Gabansa. Hoto daga @GovKaduna
Asali: Twitter

Channels TV ta rahoto cewa, Sanusi yayi wannan batun a Kaduna yayin da ake gudanar da taron shekara shekara na KadInvest wanda Cibiyar Habaka zuba Hannayen jari na jihar Kaduna ke shiryawa.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Wike Yace Ba Atiku Kadai Bane Dan Takarar PDP

Tsohon Gwamnan babban bankin Najeriyan ya jajanta yadda ake satar mai a Najeriya, karuwar bashi, tallafin man fetur da kuma lalacewar darajar kudin kasar daga cikin manyan kalubalen tattalin arzikin da Najeriya ke fuskanta a wannan lokacin.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sanusi ya kara da kira ga gwamnatocin jihohi da su kubutar da kansu daga cika dogaro da gwamnati tarayya.

“Ina cigaba da maimaitawa, ina fatan za mu tuna cewa na rasa aikina a babban bankin Najeriya saboda wannan matsalar. Ba wai saboda takamaiman jam’iyya ba. Bani da jam’iyya. Jam’iyyata ita ce Najeriya. Wannan ce matsalar da muka samu a 2014. Asiwaju Tinubu ya san Najeriya ce jam’iyyata.”

- Ya sanar yayin jawabi ga jama’a da suka hada da Tinubu.

Sanusi shi ne babban mai jawabi kan batun tattalin arziki da ake tattaunawa a wurin.

A taron, shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya samu wakilcin karamat Ministan masana’antu, cinikayya da zuba hannayen jari, Maryam Katagum.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Dalilin da Yasa Na Yi Murabus Daga Shugaban BoT Na Kasa, Jibrin Ya Fadi Gaskiya

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir Ahmad El-Rufai tare da takwaransa na jihar Kebbi, Abubakar Bagudu duk sun halarci wurin.

Dan takarar Gwamnan Kaduna ya sheke gari, ya kai wa Muhammadu Sanusi ziyara a gida

A wani labari na daban, labari ya zo mana cewa Sanatan Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa, Uba Sani ya kai ziyara ta musamman ga Muhammadu Sanusi II.

Sanata Uba Sani ya ziyarci Mai martaba Muhammadu Sanusi II ne a gidansa kamar yadda wasu hotuna da ya wallafa a shafinsa na Twitter suka nuna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel