‘Dan takarar Gwamnan Kaduna ya sheke gari, ya kai wa Muhammadu Sanusi ziyara a gida

‘Dan takarar Gwamnan Kaduna ya sheke gari, ya kai wa Muhammadu Sanusi ziyara a gida

  • Uba Sani ya kai wa Mai martaba Muhammadu Sanusi II ziyara a yammacin ranar 27 ga watan Yuni 2022
  • Ana tunani ‘Dan takarar Gwamnan na jihar Kaduna na APC ya ziyarci Khalifa Sanusi II ne a kasar waje
  • Sanata Sani ya yi farin cikin haduwarsa da tsohon Gwamnan na CBN, yace ya amfana da zamansu

Kaduna - Labari ya zo mana cewa Sanatan Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa, Uba Sani ya kai ziyara ta musamman ga Muhammadu Sanusi II.

Sanata Uba Sani ya ziyarci Mai martaba Muhammadu Sanusi II ne a gidansa kamar yadda wasu hotuna da ya wallafa a shafinsa na Twitter suka nuna.

Uba Sani yake cewa ya gana da tsohon Sarkin na Kano, kuma ya samu damar tattaunawa a kan wasu muhimman abubuwan da suka shafi al’umma.

Kara karanta wannan

Cikakken jerin Sanatoci 58 da aka zazzage, ba za su koma kujerunsu a Majalisar Dattawa ba

‘Dan takarar gwamnan jihar Kaduna ya daura hotunan ne a Twitter a ranar Litinin, 27 ga watan Yuni 2022 da kimanin karfe 10:30 (agogon Najeriya).

Da yake bayani a shafin na sa, Sani wanda zai yi wa APC takarar Gwamna a Kaduna ya bayyana Sanusi II a matsayin fitaccen masanin tattalin arziki.

Hotunan sun jawo mutane su na ta tofa albarkacin bakinsu a dandalin Twitter, sai dai ba za mu iya cewa ga inda Sanusi II ya karbi bakuncin Sani ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

‘Dan takarar Gwamnan Kaduna
Muhammadu Sanusi II tare da Uba Sani Hoto: @UbaSaniUs
Asali: Twitter

Jawabin Uba Sani

“Yau, na kai ziyara ta musamman ga Mai martaba Sarkin Kano na 14 a tarihi, Khalifa Muhammad Sanusi 11.”
“Tattaunawa ta da fitaccen masanin tattali kuma gawurtaccen masanin ya amfanar matuka, ya kara mani haske.”
“Nagode Mai martaba da wannan dama.” – Uba Sani.

NNPP ta yi kamu a Kaduna?

Kara karanta wannan

Rikicin kujerar Sanata Ahmad Lawan, ya dauki zafi, Machina ya yi wa Shugaban APC raddi

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa ana rade-radin wasu ‘ya ‘yan APC da tsofaffin jami’an Gwamnatin Nasir El-Rufai a jihar Kaduna sun koma jam’iyyar NNPP.

Daga cikin wadanda ake jita-jitar sun bar APC har da tsohon kwamishinan ilmi, Farfesa Shehu Adamu Usman, da ‘dan majalisar Zaria, Hon. Sulaiman Dabo.

Mun tuntubi Mai ba gwamnan Kaduna shawara a kan harkokin siyasa, Rt. Hon. Aminu Shagali, wanda ya karyata wannan rahotanni, ya ce ba gaskiya ba ne.

Dr. Shagali ya ce hotunan da ake yadawa wadanda aka dauka tun tuni ne, sannan ya yi watsi da ikirarin da ake yi na cewa APC na fuskantar barazana a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel