Rikicin PDP: Wike Ya Dauki Ortom, Makinde Da Ikpeazu Sun Shilla Kasar Waje, An Bayyana Dalilin Fitarsu
- Wasu jiga-jigan jam'iyyar PDP da suka kunshi Wike da na hannun damansa sun tafi Madrid, babban birnin kasar Spain, don taro mai muhimmanci
- Tawagar ta bar Najeriya zuwa Spain ne a daren ranar Juma'a 14 ga watan Oktoba, bayan ya zargi Iyorchia Ayu, shugaban PDP na kasa da rashawa.
- Ana sa ran wani cikin mamban na G5, Gwamna Ifeanyi Ugwuanyi na jihar Enugu, zai tafi ya tarar da takwarorinsa a Spain daga bisani
Kungiyar gwamnonin jam'iyyar PDP su biyar da ake kira (G5) da ke neman a yi adalci da daidaito a jam'iyyar sun tafi Spain don yin wani taro mai muhimmanci.
An tattaro cewa kungiyar karkashin jagorancin Gwamna Nyesom Wike na Jihar Rivers sun bar Najeriya don zuwa Madrid a daren Juma'a.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Sauran yan tawagar suna Gwamna Seyi Makinde (Oyo); Okezie Ikpeazu (Abia) da Samuel Ortom (Benue).
An gano cewa akwai yiwuwar Gwamna Ifeanyi Ugwuanyi na jihar Enugu zai iya bin su daga baya, The Nation ta rahoto.
G5 din sun dade suna kira cewa shugaban PDP na kasa, Dr Iyorchia Ayu ya yi murabus kafin su shiga kwamitin kamfen na dan takarar shugaban kasar jam'iyyar, Atiku Abubakar.
Gwamnonin da ke fushi sun dage cewa ba adalci bane shugaban jam'iyyar na kasa da dan takarar shugaban kasa su fito daga yanki guda daya.
Wike ya jagoranci tawagar zuwa Spain bayan hirar kai tsaye da ya yi a Port Harcourt inda ya sake yin zargi kan Ayu tare da cewa ba shi da nagarcin da zai jagoranci jam'iyyar a kamfen din 2023.
Rikcin Jam'iyyar PDP Na Nuna Wa 'Yan Najeriya Akwai Hadari a 2023, Wike
Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya ce rikicin da ya addabi jam'iyyar PDP ka iya shafar damar da take da shi na samun nasara a babban zaɓen 2023.
Daily Trust ta ruwaito gwamna Wike na cewa a halin yanzu PDP na faɗa wa 'yan Najeriya kar su kuskura su ba ta amana idan aka yi la'akari da yadda jam'iyyar ta gaza shawo kan rikicinta.
Gwamnan ya yi wannan furucin ne yayin hira da manema labarai a gidan gwamnatinsa dake Patakwal, babban birnin jihar Ribas ranar Jumu'a.
Asali: Legit.ng