2023: Sunayen Gwamnonin Kudu 4 Da Aka Tura Su Roki Nyesom Wike

2023: Sunayen Gwamnonin Kudu 4 Da Aka Tura Su Roki Nyesom Wike

  • Ana saura yan watanni zaben shugaban kasan 2023, har yanzu rikici karade jam'iyyar adawa ta PDP
  • Sakamakon wannan rikici dake gudana, ana ganin jam'iyyar APC zata lashe zabe cikin sauki
  • Jam'iyyar PDP ta aika wasu manyan gwamnonin yankin Wike don su bashi hakuri

Uyo - Gwamnonin yankin Kudu maso kudu na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) aka tura rokon gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, don ya sauka daga tudun na ki da ya hau kan shugaban uwar jam'iyyar, Iyorchia Ayu.

Wike ya lashe takobin cewa ba zai goyi bayan Atiku Abubakar ba har sai Iyorchia Ayu ya sauka daga kujerar.

A cewara rahoton The Nation, Gwamnonin da aka tura sun hada da:

  • Udom Emmanuel (Akwa Ibom);
  • Douye Diri(Bayelsa);
  • Ifeanyi Okowa (Delta)
  • Godwin Obaseki (Edo),

Kara karanta wannan

Idan Na Tona Asirin Ayu, Ko 'Yayansa Sai Sun Guje Masa: Wike

South-South
2023: Sunayen Gwamnonin Kudu 4 Da Aka Tura Su Roki Nyesom Wike
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wannan ya bayyana cikin jawabin da aka fitar bayan zaman kungiyar gwamnonin PDP na yankin kudu maso kudu da akayi a Uyo.

Gwamnan Delta, Ifeanyi Okowa, ne ya rattafa hannu kan jawabin ranar Laraba, 12 ga Oktoba,.

Yace:

"An yi zaman ne don kira ga gwamnonin PDP na yankin kudu maso kudu suyi dukkan mai yiwuwa wajen baiwa dan'uwansu Gwamna Nyeson Wike hakuri don ya hada kai da jam'iyya wajen ceto kasar nan don amfanin yan Najeriya."

Dalilin da Yasa Na Yi Murabus Daga Shugaban BoT Na Kasa, Jibrin Ya Fadi Gaskiya

Shugaban kwamitin amintattu na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Walid Jibrin, ya magantu a kan murabus da yayi daga kujerarsa.

A farkon watan Satumba ne Jibrin wanda ya kasance tsohon sanata, ya sanar da murabus dinsa a taron BoT na PDP da ya gudana a Abuja.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel