Zaben 2023: Jonathan Zai Goyi Bayan Atiku, Ya Kira Okowa Mataimakin Shugaban Kasa Mai Jiran Gado
- Daga karshe dai, tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya fito fili ya bayyana yan takarar da ya ke goyon baya a 2023
- Jonathan ya nuna cewa yana tare da jam'iyyar PDP har ma ya kira Gwamna Okowa, mataimakin shugaban kasa mai jiran gado
- Hakan ya faru ne a yammacin ranar Laraba yayin da Okowa, abokin takarar Atiku, ya jagoranci tawaga ta ziyarci Jonathan a Abuja
FCT, Abuja - Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya goyi bayan takarar shugabancin kasa na Atiku/Okowa a zaben 2023, rahoton The Cable.
Mr Jonathan ya bayyana hakan ne a yayin da tawagar PDP karkashin jagorancin dan takarar mataimakin shugaban kasa Gwamna Ifeanyi Okowa tare da Gwamna Bala Mohammed na Bauchi suka kai masa ziyara a Abuja a yammacin ranar Laraba.
Rarara Ya Caccaki Ganduje A Sabuwar Waƙa Da Ya Fitar, Lamarin Ya Haifar Da Cece-Kuce A Soshiyal Midiya
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A wani bidiyo da ya bazu a dandalin sada zumunta, GEJ a matsayinsa na tsohon shugaban kasa ya bayyana Gwamna Okowa a matsayin mataimakin shugaban kasa mai jiran gado.
Mataimakin shugabna kasa mai jiran gado, Jonathan ya kira Okowa
Jonathan ya fada wa Okowa:
"Mataimakin shugaban kasar mu mai jiran gado - ya yi wa'adi biyu a matsayin gwamna."
Mr Jonathan ya kara da cewa a shirye ya ke ya goyi baya tare da yi wa jam'iyyar PDP aiki don ganin ta yi nasara a 2023.
Hakan na nufin cewa tsohon shugaban kasa Jonathan zai goyi bayan Alhaji Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar ta PDP a 2023.
Jawabin Okowa
A bangarensa, Gwamna Okowa ya ce yana da muhimmanci a nemi goyon baya da albarka daga tsohon Shugaba Jonathan, kuma da albarkarsa jam'iyyar za ta yi nasara a Fabrairu.
Ya ce Jonathan yana da halayen ainihin dattijon kasa, ya kara da cewa sun kai ziyarar ne don tattauna halin da kasa ke ciki da shirin yadda za a ceto kasar a sake gina ta.
Asali: Legit.ng