Ana Rigima a Jam’iyyar APC Tun da Ministan Buhari Ya Ki Fitowa Ya Goyi Bayan Tinubu

Ana Rigima a Jam’iyyar APC Tun da Ministan Buhari Ya Ki Fitowa Ya Goyi Bayan Tinubu

  • Basil Ejidike ya yi raddi ga Ministan kwadago, Chris Ngige a dalilin kin tallata masu Bola Tinubu
  • Duk da yana APC, tsohon gwamnan ya ki fadin wanda zai zaba tsakanin Tinubu da Peter Obi a 2023
  • Wannan ya jawo ana musayar kalamai tsakanin bangarorin APC na su Basil Ejidike da Emeka Ibe

Anambra - Jam’iyyar APC ta reshen jihar Anambra ta nesanta kanta daga Chris Ngige saboda ya ki tallata Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a gaban Duniya.

Daily Trust ta fitar da rahoto da yace APC ta nuna babu ruwanta da Ministan kwadago saboda rashin goyon bayan ‘dan takaranta na shugaban kasa.

Shugaban APC a Anambra, Basil Ejidike ya barrantar da jam’iyya mai mulkin kasar daga Dr. Chris Ngige bayan wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin.

Kara karanta wannan

Bayan An Kai Ruwa Rana, Gwamna Wike Ya Yarda Zai Marawa Atiku Baya da Sharadi

Cif Basil Ejidike yace babu ruwan jam’iyyar APC da ra’ayin Ngige wanda ya ki nuna fifiko tsakanin Bola Tinubu da Peter Obi mai takara a jam'iyyar hamayya.

Okelo Madukaife 'dan zagon-kasan APC ne

Baya ga Ministan, Ejidike ya kuma nuna damuwarsa a kan Okelo Madukaife wanda ya taba zama sakataren yada labaran jam’iyyar APC na reshen Anambra.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban jam’iyyar ya zargi Okelo Madukaife da yi wa APC zagon-kasa, yake cewa ‘dan siyasar yana yawo yana cewa shi ne mai magana da yawun bakinsu.

Magoya Bayan Tinubu
'Yan takara da jiga-jigan APC Hoto: @officialasiwajubat
Asali: Facebook

Dailypost ta rahoto Ejidike yana cewa tun shekarar 2021 aka maye gurbin Madukaife da Valentine Oliobi, wanda shi ne yake magana da yawun bakin jam'iyya.

Ana haka kuma sai ga wani rahoto daga Mista Emeka Ibe yana maida martani ga bangaren Ejidike. Ibe ne shugaban ‘yan taware na APC a jihar ta Anambra.

Kara karanta wannan

Atiku Abubakar Ya Kinkimo Manya 3 Domin Su Lallabi Wike Ya Marawa PDP baya

Emeka Ibe ya fitar da jawabi yana cewa tsaida Ahmed Bola Tinubu a matsayin ‘dan takarar shugaban kasa, ya taimaka wajen kara barka jam'iyya ta reshensu.

Jagoran ‘yan tawaren ya kare Ngige daga zargi, yake cewa tun farko Ministan bai shaidawa jama'a cewa yana wakiltar APC a lokacin da aka zauna da shi ba.

Emeka Ibe yace shi ne shugaban APC

Shi kuwa Emeka yace Ejidike ba ainihin ‘dan jam’iyya ba ne, kuma bai da hurumin da zai yi magana a madadinsu domin kotu ta tabbatar da shi yake rike da APC.

A cewar Ibe, hukuncin kotun daukaka kara da ke zama a Enugu na kwanaki ya tabbatar da cewa ‘yan bangarensa ne asalin shugabannin APC ba su Ejidike ba.

Kotu ta Rusa Lissafin ‘Dan Takara

Mun ji labari cewa dole Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta sake shirya zaben wanda zai yi takarar 'Dan majalisar wakilan tarayya a mazabar Akoko.

Kara karanta wannan

Akwai Adalci a PDP Sabanin APC: Gwamna Tambuwal Ya Bayyana Bambancin Manyan Jam’iyyun Siyasar Kasar 2

Dr. Victor Ategbole ya yi nasara a karar da ya shigar da INEC da jam’iyyarsa mai mulki, an rugaza zaben da ya ba Adegboyega Asiwaju Adefarati nasara a Ondo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel